Kasuwanci
Gwamnatin Neja Ta Haramta Karbar Haraji A Hannun Masu Kananan Sana’o’i
Gwamnatin jihar Neja ta haramta wa masu tattara kudaden shiga a fadin kananan hukumomi ashirin da biyar na jihar karbar haraji daga hannun ‘yan talla da masu kananan sana’o’i.
Gwamnan jihar Mohammed Umar Bago ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamnati Minna, babban birnin jihar.
Mohammed Umar Bago wanda ya yi Allah-wadai da yadda ake karbar kudade ba bisa ka’ida ba a hannun kananan ‘yan kasuwa, ya umurci shugabannin kananan hukumomi da kansiloli da su kara sa ido tare da tabbatar da ganin an kawo karshen irin wadannan ayyuka nan take.
Ya tunatar da su cewa gwamnatin jihar Neja tana da tsarin bai daya da ya hana karbar haraji dafa masu kananan sana’o’i domin basu damar dogaro da kai.
“Mun yanke shawarar cewa daga yanzu, babu wwanimai karamar sana’a da za a sake karbar haraji a hannunsa a wannan jihar.”
“’Yan talla da kananan ‘yan kasuwa ba sa biyan haraji a Jihar Neja, kuma duk wanda aka samu yana karbar haraji daga wurinsu zai dandana kudarsa,” inji Gwamnan.
Daga Aliyu Lawal
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai24 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
