Connect with us

Nishadi

Murja Ta Kai Ƙarar Hisbah Gaban Kotu

Published

on

 

Fitacciyar jarumar nan ta dandalin TikTok, Murja Ibrahim Kunya, ta yi ƙarar Gwamnatin Kano a gaban Babbar Kotun jihar.

Wannan dai na cikin ƙunshin takardar ƙarar da Murja ta shigar bisa wakilcin lauyoyinta — A. U Hajji da S.S Shehu — mai ɗauke da kwanan watan 26 ga Fabarairun 2024.

A ƙunshin ƙarar da Magatakardan Kotun, Adam S. Adam ya rattaba hatimi da kuma sa hannu, Murja ta buƙaci a shiga tsakaninta da Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kwana Huɗu.

Aminiya ta ruwaito cewa, cikin jerin waɗanda ƙarar da Murja ta shigar ta shafa akwai Antoni-Janar na Jihar Kano da Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, da Hukumar Hisbah da Hukumar Asibitocin Kano da Babban Asibitin Masu Larurar Kwakwalwa da ke Dawanau.

Takardar ta nuna cewa, Babbar Kotun ta cimma muradu huɗu daga cikin jerin buƙatu bakwai da lauyoyin Murja suka gabatar wa Mai Shari’a Nasiru Saminu.

Sai dai Aminiya ta lura cewa, daga cikin buƙatun lauyoyin Murja da kotun ta yi watsi da su, har da ta neman mayar wa wadda suke wakilta wayarta ta hannu kirar iPhone da kuma katin banki na ATM.

Da wannan hukuncin ne kotun ta kuma ɗage ƙarar zuwa 20 ga watan Maris na 2024.

Ana iya tuna cewa, a bayan nan dai Mai Shari’a Malam Nura Yusuf Ahmad na Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kwana Huɗu ya bayar da umarnin a yi wa Murja gwajin kwakwalwa.

Mai Shari’a Nura Yusuf ya ba da umarnin yi wa Murja gwajin kwakwalwar ne a asibitin gwamnati domin tabbatar da ƙoshin lafiyarta

Alkalin ya ba da umarnin ne bisa zargin jarumar ba ta cikin hayyacinta a lokacin zaman kotun na farko da aka gurfanar da ita.

Tun farko dai Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ce ta gurfanar da Murja kan zargin tayar da hankalin jama’a, bata tarbiyya da kuma koyar da karuwanci.

Labarai

Labarai20 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai22 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara