Labarai
Zanga-Zanga: NLC Ta Damka Wa Majalisa Jerin Bukatun ’Yan Najeriya
Shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero, ya damka wa majalisar dokoki ta kasa kundin bukatun al’ummar Najeriya zuwa ga gwamnatin tarayya.
Bukatun da Ajaero ya damka a hannun shugaban Kwamitin Kwadago da Samar da Ayyuka na Majalisar Dattawa, Sanata Diket Plang, sun hada da aiwatar da daukacin bukatun kungiyar kan jin dadin ma’aikata da kuma samar da ayyukan yi ga ’yan kasa.
Sauran su ne, gyara matatun man gwamnati guda hudu da ke kasar da kuma ba wa manoma tallafin noma ba tare da bata lokaci ba, domin saukaka samar da abinci a kasa.
Kwamred Ajaero ya shaida wa Sanata Diket Plang ranar Talata cewa al’ummar Najeriya suna gudanar da zanga-zangar lumanar ce saboda yunwar da ke addabar su, inda ya kwatanta halin da kasar ta tsinci kanta da na kasar Zimbabwe.

Shugaban na NLC ya ce zanga-zangar za ta farkar da gwamnati wajen hanzarta yin abin da ya kamata domin shawo kan matsalolin da ke ci wa kasar tuwo kwarya.
A cewarsa, bangarensu da na gwamnati sun riga sun fara tattaunawa kan batun mafi karancin albashi, amma ba su kai ga cim-ma matsaya ba.
A nasa bangaren, Sanata Plang ya ba su tabbacin tattauna bukatun masu zanga-zangar da nufin ganin an yi abin da ya dace.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
