Kasuwanci
Bankin CBN ya Kayyade Yadda za a Rika Sayar da Dala
Babban Bankin Najeriya ya kayyade wa ’yan canji yadda za su rika sayar da Dala, da kuma ribar da za su dora.
A ranar Talata babban bankin ya sanar da hakan tare da cewa zai rika ba wa kowane dan canji mai rajista kudaden kasashen waje da kimarsu ta kai Dala N20,000 a kan kowace Dala, N1,301.
“Ribar da za su dora ba zai haura kashi daya cikin 100 na farashin da suka samu kudaden kasashen wajen daga hannun CBN ba,” in ji sanarwar mai dauke da sa hannun Daraktan Kasuwanci da Musayar Kudade na CBN, Hassan Mahmud.
Hakan na zuwa ne kimanin shekaru biyu da CBN, a karkashin jagorancin tsohon shugabanta, Godwin Emefiele, ya dakatar da ba wa ’yan caji kudaden kasar wajen.
Amma sabuwar sanarwar ta ce bankin ya lura tsohon tsarin ya haifar da tazara mai yawa a farashin Dala a hukumance da kuma a wurin ’yan canji.
A cewar sanarar, ana sa ran sabon matakin ba wa ’yan canji Dala zai hana tashin gwauron zabon da take yi da kuma rage bambancin tsakanin farashin gwamnati da na ’yan canji.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
