Connect with us

Labarai

Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa A Jigawa

Published

on

 

Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya kaddamar da hukumar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa a jihar.

Yayin jawabinsa a wajen bikin kaddamar da hukumar, Gwamna Umar Namadi ya jaddada mahimmancin  hukumar wajen  yaki da cin hanci da rashawa domin tsaftace ayyuku a jihar.

Ya kuma bukaci mambobin hukumar da su yi aiki bisa doka ba tare da tsoro ko nuna son kai ba.

“Kada ku bari bukatun ku su yi tasiri a ayyukanku, haka kuma babu wanda zai tsoma baki cikin ayyukanku daga bangaren gwamnati.” Inji Gwamnan

Malam Umar Namadi ya kuma bukaci hukumar da ta kiyaye ka’idojin aiki, tare da yin  adalci dm wajen magance korafe-korafen da aka kawo mata.

A jawabinsa, shugaban  hukumar Barista Salisu Abdu, ya nuna jin dadinsa ga Gwamna Namadi bisa bashi damar jagorantar hukumar.

Ya kuma tabbatar wa da al’umma kudurin hukumar na tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen gudanar da ayyukanta.

Hukumar za ta tabbatar da manufar Gwamna Namadi na samar da sabuwar Jihar Jigawa ba tare da cin hanci da rashawa ba, mun yi alkawarin yin aiki bisa gaskiya da amana ba tare da son zuciya ba.”

Gidan Rediyon Najeriya Kaduna ya ruwaito cewa, an dorawa  hukumar korafe-korafen al’umma da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar alhakin binciken  ma’aikatu da hukumomin gwamnati na jiha da kananan hukumomi da ma ma’aikatan jihar baki daya.

An rantsar da sabon shugaban hukumar Barista Salisu Abdu tare da sauran mambobin hukumar na dindindin da suka hada da Musa Kallamu Uba Auyo da Hassan Hashim, a zauren majalisar da ke gidan gwamnati a Dutse.

 

Usman Muhammad Zaria

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara