Labarai
Gwamnatin Sakkwato Ta Kashe Kusan Naira Biliyan 2 Wajen Sayen Gidaje
Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya shawarci gwamnonin jihohi 36 na tarayya da su ba da fifiko kan samar da abinci domin dakile matsalolin da ‘yan Najeriya ke fuskanta.
Obasenjo ya ba da wannan shawarar ne a jihar Sokoto yayin da yake kaddamar da wasu gidaje 136 da gwamnatin jihar Sokoto ta saya a kan kudi naira miliyan dubu daya da miliyan dari takwas da ashirin.
Tsohon shugaban kasar wanda ya kai ziyarar kwanaki 2 a jihar Sokoto, ya bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a halin yanzu ya kawo cikas ga ci gaban zamantakewa da tattalin arziki da tsaro a kasar nan.
Ya kara da cewa, a matakin tarayya da na jihohi, dole ne shugabanni su yi kokarin canza yanayin wahalhalun da ake ciki da nufin tabbatar da amanar da aka yi masu.
A cewar Obasanjo wanda ya kuma amince da gagarumin ci gaban da gwamna Ahmed Aliyu ke samu a fannin sufuri, gina tituna da ayyukan gidaje, ya bayyana shi a matsayin jajirtaccen shugaba wanda yayi tsayin daka da ayyukansa da za su sake dawo da ci gaban ababen more rayuwa a jihar.
Tsohon shugaban kasar ya kuma yabawa Sanata Aliyu Wamakko da mai alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar bisa irin gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban jihar .
Tun da farko Gwamna Ahmad Aliyu Sokoto ya ce tunanin samar da ayyuka da dama na gidaje ya dace da alkawuran yakin neman zabensa na aiwatar da ayyukan da suka shafi dan Adam da za su tabbatar da jin dadin jama’a da martabar al’ummar jihar.
A cewar gwamnan gwamnatin jihar ta sadaukar da makudan kudade wajen ginawa tare da kammala sauran ayyuka makamantan haka a fadin jihar da suka hada da shirye-shiryen karfafa matasa da samar da asibitoci na zamani da kayayyakin kiwon lafiya.
NASIR MALALI/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
