Labarai
Kungiyar CAN Ta Rasa Mata Shida A Hadarin Mota A Taraba

An bayyana cewa wasu ’yan kungiyar mata ta kungiyar Kiristoci ta Najeriya (WOWICAN) su shida ne suka rasa rayukansu a wani hadarin mota da ya rutsa da su a jihar Taraba.
Hadarin ya afku ne a lokacin da suke dawowa daga taron kungiyar mata ta CAN wanda ya gudana a Gembu, karamar hukumar Sardauna ta jihar a ranar 18 ga watan Mayu, 2024.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai baiwa gwamna Agbu Kefas shawara kan harkokin yada labarai da sadarwa na zamani, gwamna Kefas ya bayyana matukar bakin cikinsa da faruwar lamarin, inda ya bayyana lamarin a matsayin wata bakar lahadi ga jihar.
Ya jajantawa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, ya kuma ba da tabbacin samar wa jama’a hanyoyin tsaro.
Sanarwar ta bayyana cewa, gwamnan ya umarci shugabannin kananan hukumomin da su tabbatar da kula da hanyoyin da ake da su, da suka hada da na’urorin kula da ababen hawa, da magudanar ruwa, da kuma gyaran ababen more rayuwa, domin hana afkuwar irin wannan bala’i a nan gaba.
Gwamna Kefas ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga shugabancin CAN, WWICAN, da daukacin al’ummar Kirista a jihar da ma kasa baki daya.
Sani Sulaiman/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
