Labarai
An Kwashe Mutane Da Dama Bayan Mummunar Ambaliyar A China
Hukumomi sun kwashe kimanin mutune dubu sittin daga gidajensu da ke Guangdong, yayin da mamakon ruwan saman da aka shafe kwanaki ana yi ya janyo ambaliyar ruwa a lardin da ke da mafiya yawan al’umma a China.
Mutune 11 ne suka yi ɓatan dabo sai dai ba a bayar da rahoton asarar rai ba.
Bidiyo daga kafafen yaɗa labaran ƙasar sun nuna yadda ambaliyar ruwan ta shafe wurare, inda kuma masu aikin ceto cikin kwale-kwale ke kwashe mutane daga ruwan da tsayinsa ya kai ƙugunsu.
Manyan kogunan ƙasar sun tumbatsa sannan hukumomi suna sa ido kan lamarin.
A sassan lardin, kusan gidaje sama da miliyan daya ne suka faɗa cikin duhu a karshen mako, amma an gyara wutar kashi 80 cikin 100 na gidajen ranar Lahadi da daddare.
An soke tashin jirage, wasu kuma an jinkirta lokacin tashin su a filin jirgin saman Baiyun da ke Guangzhou saboda ruwan daka ayi ta zabgawa, yayin da kuma aka buƙaci makarantu a birane aƙalla uku su rufe.
Gidaje da dama a sassan lardin ko dai sun ruguje ko kuma sun gamu da ɓarna mai girma, inda hukumomi suka ƙiyasta cewa tattalin arziki ya yi asarar kusan Dala Miliyan goma sha tara da miliyan dari tara.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
