Labarai
An Nada Sarkin Dass A Matsayin Amirul Hajji Na Jihar Bauchi
Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na jihar Bauchi ya amince da nadin Sarkin Dass Alhaji Usman Bilyaminu Othman, a matsayin Amirul Hajji na Jahar don gudanar da aikin Hajjin 2024 a kasa mai tsarki.
Wasikar nadin mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Barista Ibrahim Mohammed Kasim na nuni da cewa nadin nasa tare da wasu fitattun ‘yan jihar 13, an yi sa ne bisa jajircewar su da sadaukar da kai, da kiyaye dokokin Allah Madaukakin Sarki.
Gwamna Bala Mohammed ya bayyana kwarin guiwar tawagar da aka nada, inda ya jjaddada cewa yana da yakimin za su yi aiki yadda yakamata.Ya nanata kudurin gwamnatin jihar na tallafawa alhazai da kuma tabbatar da jin dadin su a tsawon tafiyarsu.
Sauran membobin tawagar ta Amirul Hajj sun hada da mataimakin shugaban majalisar jihar Honarabul Jamilu Umar Dahiru a matsayin mataimakin Amirul Hajj,da mai shari’a Rabi Talatu Umar, Babbar Alkalin Jihar Bauchi, da
Khadi Umar Ahmed Liman, da Honarabul Yakubu Ibrahim Hamza, da kuma Honarabul.
Sauran sun hada da Alhaji Ibrahim Y.M Baba Hakimin Yelwan Duguri, da Galadiman Bauchi Surv. Ibrahim Saidu Jahun, da Alhaji Yayanuwa Zainabari
da Sheikh Zubairu A. Madaki, da kuma Sheikh Salisu Sulaiman Ningi.
Har ila yau akwai Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi, da Malam Ahmad Inuwa Na’ibi, da kuma Muhammad Haruna Barde a matsayin sakataren tawagar.
Tawagar za ta yi aiki tare da hukumomin da abin ya shafa da suka hada da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jiha, da Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) da kuma Gwamnatin Saudiyya, domin tabbatar da ganin an samu nasarar gudanar da aikin hajjin bana ga daukacin alhazan Jihar Bauchi.
Gwamnan ya bukaci tawagar da aka nada da ta bada himma wajen gudanar da ayyukanta, tare da tabbatar da bin gaskiya da adalci.
-
Labarai4 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai5 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai5 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai5 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai4 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai3 days agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai2 days agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
-
Labarai3 days agoShugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus
