Connect with us

Labarai

Sanata Barau Ya Kai Ziyarar Gani Da Ido Aikin Da Ake Yi A AKTH

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada kudirinta na inganta harkar kiwon lafiya a fadin kasar nan, daidai da manufar sabunta kudiri na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wato Renewed Hope Agenda.

Wannan tabbacin ya fito ne daga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, yayin da yake ziyarar duba ayyukan gine-gine da ke gudana a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), wanda shi ne ya tallafa wajen samar da su.

Yayin da yake magana da ’yan jarida a lokacin ziyarar, Sanata Barau ya ce wadannan ayyuka na da nufin kara karfin cibiyoyin kiwon lafiya a cikin gida, tare da rage yawan tafiyar da ake yi zuwa kasashen waje domin neman magani, ta hanyar samar da ingantattun kayan aiki a asibitocin cikin gida.

Wadannan shirye-shirye suna cikin cikakkiyar manufa ta Shugaba Tinubu ta farfado da sashen kiwon lafiya,” in ji shi. “Nigeria na da kwararrun ma’aikatan lafiya, kuma idan aka samar musu da ingantattun kayan aiki, za a karfafa gwiwarsu, kuma za mu iya cimma burin kasa wajen ingantaccen tsarin kiwon lafiya.”

Dan majalisar ya kara da cewa, idan an kammala wadannan ayyuka, za su taimaka wajen kara ingancin ayyukan asibitin, tare da bai wa jama’a damar samun kulawar lafiya ta zamani da inganci.

A nasa bangaren, Babban Daraktan Asibitin, Farfesa Abdulrahman Sheshe, ya nuna godiya bisa wannan taimako, yana mai cewa ayyukan suna tafiya yadda ya kamata, kuma ana sa ran kammalawa da kaddamar da su kafin shekarar 2026.

A cewarsa, ayyukan sun hada da gina Cibiyar Nazarin Cutar Zuciya da Kwakwalwa (Cardio-Cerebral Center), Cibiyar Kula da Yara (Pediatric Center), da masaukan daliban jinya, da sauran muhimman gine-gine.

Wadannan sabbin cibiyoyi za su kara yawan gadon marasa lafiya, kuma za su ba mu damar gudanar da ayyukan da ba mu iya yi ba a baya,” in ji Farfesa Sheshe.

Ya kara da cewa, sabbin cibiyoyin za su kara ingancin ayyuka, tare da karfafa matsayin asibitin wajen zama jagora a harkar kiwon lafiya a yankin.

 

Abdullahi Jalaluddeen

Labarai

Labarai20 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai22 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara