Fasaha
Najeriya Ta Karɓo Rancen Dala Biliyan 1.3 Don Kammala Layin Dogon Kano Zuwa Maraɗi
Gwamnatin Najeriya ta karɓo rancen dala biliyan 1.3 domin kammala aikin titin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Maraɗi da ke Jamhuriyyar Nijar.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin sanarwar da Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya ta yi a ranar Laraba.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa kamfanin gine-gine na ƙasar China, CCECC, ne zai samar da kaso 85 na kuɗaɗen da ake buƙata.
Haka kuma, ma’aikatar ta ce Gwamnatin Najeriya da haɗin gwiwar Bankin habaka tattalin arzikin Afirka na Africa Development Bank ne ke ɗaukar nauyin aikin.
“Samun bashin na dala biliyan 1.3 na nuna irin nasarar da za a samu wajen kammala layin dogon,” in ji sanarwar.
Wannan dai na ɗaya daga cikin shirye-shiryen Gwamnatin Najeriya na inganta harkar sufuri a faɗin ƙasar domin bunkasa tattalin arziki da ke fama da masassara.
-
Labarai5 days ago
Jirgin Farko Na Alhazan Najeriya Ya Tashi Zuwa Kasa Mai Tsarki
-
Ilimi6 days ago
Gwamnatin Jigawa Ta Bada Kwangilar Hanyar Kiyawa Zuwa Birnin Kudu
-
Fasaha6 days ago
Kasuwar Panteka Ta Kaduna Ta Samu Lasisin Koyar Da Sana’o’i —NBTE
-
Labarai6 days ago
Sheikh Bin Uthman Ya Jaddada Muhimmancin Rikon Amana Ga Jami’an Hukumar Alhazai
-
Labarai4 days ago
Majalisar Dattijan Na So A Bai Wa Kananan Hukumomi Yancin Kai
-
Labarai6 days ago
Gwamnatin Kano Ta Nada Ibrahim Garba Shugaban Tawagar ‘Yan Jarida A Hajjin Bana
-
Labarai6 days ago
Jamhuriyar Benin Ta Haramta Fitar Da Masara Zuwa Nijar
-
Labarai6 days ago
Varane zai bar Manchester United