Ilimi
Gwamna Lawal Ya Nada Sabon Shugaban Jami’ar Jihar Zamfara
Daga Aminu Dalhatu
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da naɗin Farfesa Ibrahim Abdullahi Tsafe a matsayin sabon Shugaban Jami’ar Jihar Zamfara da ke Talata Mafara (ZAMSUT), na wa’adin shekara biyar kacal.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Abubakar Mohammad Nakwada ne ya sanar da wannan naɗin ta hannun Babban Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Sulaiman Ahmad Tudu.
Ya bayyana cewa naɗin ya biyo bayan shawarwarin Majalisar Gudanarwar Jami’ar.
Farfesa Tsafe fitaccen malami ne wanda ya samu digirin Digirgir (PhD) a shekarar 2006, kuma Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto (UDUS) ta ɗaga shi zuwa matsayin Farfesa a shekarar 2013.
Ya rike mukamai daban-daban na gudanarwa, ciki har da zama shugaban Tsangayar Nazarin Halittu da Sinadarai a UDUS. Haka kuma, ya yi aiki a matsayin Visiting Professor a ZAMSUT tun shekarar 2018, kuma a halin yanzu shi ne shugaban tsangayar kimiyya a jami’ar.
Gwamna Lawal ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa Farfesa Tsafe zai yi amfani da ƙwarewarsa da gogewarsa wajen ɗaga darajar Jami’ar ZAMSUT zuwa matsayi mafi girma, bisa manufar gwamnatinsa ta bunƙasa ilimi da nagartar karatu.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
