Labarai
NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
Daga Aminu Dalhatu, Gusau
Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru 58, Emmanuel Okonkwo, bisa zargin yin safarar wiwi, tramadol, diazepam da sauran ƙwayoyin da doka ta hana.
An kama wanda ake zargin ne a ranar 10 ga watan Satumba, 2026, da misalin ƙarfe 11:30 na dare, a shagonsa da ke yankin Bakin Tasha, Ƙaramar Hukumar Birnin Magaji ta jihar.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, ASCI Umar Mohammad, ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da wanda ake zargin tare da wasu waɗanda ake zargi da aikata laifuka a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
A cewarsa, binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya shafe sama da shekaru 20 yana gudanar da wani shagon sayar da magunguna a Birnin Magaji.
Ya ce wanda ake zargin ya amsa cewa ya haɗa baki da wasu mutane biyu, waɗanda ake kira Yellow da Sadiq, waɗanda a yanzu haka suke tsere, wajen safarar ƙwayoyin maye masu haɗari.
Kayayyakin da aka ƙwato daga hannunsa sun haɗa da fakiti 112 na wiwi, allunan Exol 5 guda 1,160, sachet 14 na tramadol da allunan Diazepam D10 guda 133.
NSCDC ta ce an miƙa wanda ake zargin ga Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa, NDLEA, domin ci gaba da gudanar da bincike da ɗaukar matakin da ya dace.
A wani labarin kuma, rundunar ta kama wasu mutane tara bisa zargin haɗa baki wajen aikata laifi, lalata dukiyar jama’a, barna da kuma satar kayan rufin makaranta daga Makarantar Firamare ta Tsageru da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe.
Umar Mohammed ya bayyana cewa Sakataren Ilimi na Ƙaramar Hukumar Tsafe, Abdulrahman Aliyu, ne ya kai rahoton lamarin ga rundunar.
Rundunar ta ce an kama wanda ake zargi da jagorantar aikata laifin, Haruna Amadu, mai shekaru 55, ɗan ƙauyen Tsageru, a ranar 8 ga watan Satumba, 2026, da misalin ƙarfe 3 na rana. Daga nan ne bincike ya kai ga gano tare da kama wasu mutane takwas da ake zargi da hannu a lamarin.
Ana zargin mutanen da haɗa baki wajen cire kayan rufin makarantar ba tare da izinin Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ba.
Rundunar ta ce waɗanda ake zargin sun kuma yi ƙoƙarin shawo kan hakiman gunduma da na ƙauye domin su ba su damar shiga harabar makarantar da kwashe kayan, amma shugabannin gargajiyar sun ƙi amincewa da buƙatarsu, tare da ba su shawarar su daina aikata hakan.
Fassara; Shafii Abubakar Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai7 days agoGwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
