Labarai
Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
Daga ALI MUHAMMAD RABIU
Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara gudanar da sa ido da tantance ayyukan waɗanda suka amfana da Asusun, bayan raba musu kuɗaɗen tallafin a cikin al’ummomi 10 na jihar.
Da yake magana kan aikin, jami’in kula da Asusun, Salihu Hussain, ya ce al’ummomin da suka amfana sun haɗa da Adewole, Warah, Afon, Oke-Ogun, Iponrin, Tsaragi, Shonga, Lafiagi, Lade da Patigi, waɗanda aka zaɓo daga wuraren da shirin ke gudanar da ayyukansa.
Ya ce waɗanda suka amfana sun bayyana cewa tallafin ya ƙara yawan ayyukan noma, ya faɗaɗa girman gonakinsu, tare da ba su damar ɗaukar ƙarin ma’aikata.
Hussain ya bayyana cewa manufar aikin sa ido ita ce tantance yadda waɗanda suka amfana suka yi amfani da kuɗaɗen da aka raba musu, da kuma duba tasirin farko da tallafin ya yi ga rayuwarsu, gano ƙalubalen da suke fuskanta da kuma ba su shawarwarin da suka dace domin tabbatar da dorewar shirin.
Ya ce KWACReSAL ya aiwatar da rabon kuɗaɗen Asusun a baya-bayan nan, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa juriyar tattalin arzikin al’umma masu rauni, musamman mata, matasa, manoma da ƙungiyoyin al’umma masu sha’awa, CIGs.
Jami’in ya ce a matakin farko, shirin ya shafi ƙungiyoyin CIG guda 50, waɗanda suka ƙunshi kusan mutum 1,000 da za su amfana, yayin da aka tanadi damar ƙara yawan waɗanda za su amfana yayin da shirin ke ci gaba.
Ya ce an tsara kuɗaɗen tallafin ne a matsayin rance, inda ake buƙatar waɗanda suka amfana su mayar da kuɗin cikin lokacin da aka amince da shi, domin sauran al’umma su samu damar cin gajiyar shirin daga baya.
Hussain ya ce tallafin ya bai wa waɗanda suka amfana damar faɗaɗa gonakinsu da noma filaye masu girma, wanda ya samar da damar shuka amfanin gona mai yawa a wannan kakar.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka amfana, Kayode Musa na ƙungiyar Agbenise Cooperative Society da ke Afon, ya ce tallafin ya ba su damar faɗaɗa harkokin noma fiye da yadda suke yi a baya, tare da ƙara shiga harkar kiwon dabbobi, inda ya ce yana kiwon kaji.
Shi ma wani wanda ya amfana, Isiaka Yakubu na ƙungiyar Ounje Lawo Cooperative Farming da ke Afon, ya ce faɗaɗa gonakin ya samar da damar ɗaukar ƙarin ma’aikata da za su yi aiki a gonakin.
Wani wanda ya amfana, Isiaka Sulaiman na ƙungiyar Ifesowapo Community da ke Gbago, ya ce shirin ya ƙarfafa ’yan ƙungiyar wajen yin aiki tare da kuma tsara makomarsu.
Ya ce tallafin ya ba su fata tare da ƙarfafa su wajen haɗa kai. Ya ƙara da cewa sun fahimci cewa idan suka kula da kuɗin yadda ya kamata kuma suka mayar da shi kamar yadda aka tsara, sauran jama’ar al’ummarsu za su samu damar cin gajiyar shirin.
Wata manomiya, Akinsola Princess, daga ƙungiyar Ifesowapo Cooperative Farming da ke Oke-Ogun, ta ce wannan kakar ta banbanta matuƙa, saboda tallafin da suka samu ya ba ƙungiyar damar faɗaɗa gonakinta, ɗaukar ƙarin ma’aikata da kuma sa ran samun amfanin gona mai yawa.
Ta yaba wa KWACReSAL kan tallafin, inda ta ce tallafin ba wai kawai ya bunƙasa harkokin nomansu ba ne, har ma ya samar da damar ayyukan yi ga wasu ’yan al’umma.
Fassara: Shafii Abubakar Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
