Labarai
Jami’an Tsaro Sun yi Nasarar Hallaka ‘Yan Bindiga 6 a Zamfara
Daga Aminu Dalhatu
Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Zamfara tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun yi nasarar dakile wani hari da ’yan bindiga suka kai garin Kanoma da ƙauyen Gidan Daji da ke Ƙaramar Hukumar Maru ta jihar.
A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, DSP Yazid Abubakar ya fitar, ya ce jami’an tsaron haɗin gwiwa sun gwabza mummunan fada da maharan, inda suka kashe shida daga cikinsu.
Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a ranar Talata da misalin ƙarfe 11 na safe, lokacin da dimbin ’yan bindiga dauke da manyan makamai da suka hada da rokoki masu linzami (RPG), manyan bindigogi masu sarrafa kansu (GPMG), bindigogin harba jiragen sama da kuma bindigogin AK-47 suka mamaye yankunan.
Bayan samun kiran gaggawa, rundunar haɗin gwiwa da ta kunshi jami’an ’yan sanda na musamman daga sashen Maru, sojoji na rundunar Operation Fansar Yamma, jami’an Sashen Yaki da Manyan Laifuka (VCRU) da kuma ’yan sa-kai sun yi gaggawar kai dauki karkashin jagorancin DPO na yankin.
Sanarwar ta bayyana cewa jami’an tsaron sun yi nasarar fatattakar maharan tare da tilasta musu ja da baya.
Ta kuma nuna cewa yayin musayar wuta, an kashe ’yan bindiga shida da ke kan babura biyu, yayin da wasu da dama suka tsere zuwa cikin dazuka da raunukan harbin bindiga.
Haka kuma, an ƙara yawan jami’an tsaro a yankin tare da ƙaddamar da sintiri mai ƙarfi domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa da kuma farautar waɗanda suka tsere.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta sake jaddada kudirinta na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da kira ga mazauna yankin da su kasance masu sanya ido tare da ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai a kan lokaci.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
