Labarai
Jihar Jigawa Ta Kammala Shirye-shiryen Dawowa da Alhazai Daga Saudiyya
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Jigawa ta bayyana cewa ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace domin dawo da Alhazan jihar daga ƙasar Saudiyya zuwa gida Najeriya.
Babban Daraktan hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan a wata hira da wakilin Rediyon Najeriya a Makkah.
Ya ce za a fara jigilar rukuni na farko na Alhazan ne ta kamfanin jirgin saman Umza daga Filin Jirgin Sama na Sarki Abdulaziz da ke Jiddah zuwa Filin Jirgin Sama na Nuhu Muhammadu Sunusi da ke Dutse a ranar 6 ga watan Yunin 2026.
A cewarsa, jirgi na biyu zai tashi a ranar 7 ga watan Yunin 2026, tare da Amirul Hajj na jihar, da wasu jami’an cibiyoyi, da ma’aikatan lafiya da kuma wasu daga cikin jami’an hukumar.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce hukumar ta samu gagarumar nasara wajen wayar da kan Alhazan da kuma ilmantar da su a lokacin zamansu a ƙasar Saudiyya.
Ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, da Hukumar Alhazai ta Lasa NAHCON, tare da Alhazan jihar bisa goyon baya da haɗin kan da suka bai wa hukumar yayin gudanar da aikin Hajjin bana.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
