Labarai
Hajj2026: Gwamna Namadi Ya Raba Goron Sallah ga Alhazan Jigawa
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bai wa kowane Alhajin jihar da ya je aikin Hajjin shekarar 2026 goron Sallah na Riyal 100 na Saudiyya.
Amirul Hajj na Jihar Jigawa kuma Sarkin Dutse, Mai Martaba Alhaji Hamim Nuhu Muhammadu Sunusi ne ya bayyana hakan yayin ziyarar Sallah da ya kai masaukin Alhazan jihar da ke Makkah.
Sarkin ya bayyana cewa kowane Alhaji daga jihar zai karɓi Riyal 100 a matsayin goron Sallah daga Gwamna Umar Namadi.
Ya ce wannan kyauta na da nufin tallafa wa Alhazan jihar ta fuskar kuɗi yayin da suke shirin dawowa gida bayan kammala ayyukan Hajjin shekarar 2026.
Da yake yaba wa Alhazan kan halayensu na gari, Alhaji Hamim Nuhu Muhammadu Sunusi ya jinjinawa yadda suka gudanar da al’amuransu tun daga zamansu a Madina, Mina, Muzdalifah da kuma Makkah.
Ya bayyana gamsuwarsa cewa babu wani daga cikin Alhazan da aka samu da laifin karya dokoki da ƙa’idojin da hukumomin Saudiyya suka gindaya.
Haka kuma, ya yaba wa Darakta Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo, da sauran jami’an gudanarwa da malamai masu wa’azi bisa shirye-shiryen ciyarwa, masauki da kuma jagorancin da suka bai wa tawagar Alhazan Jigawa a Saudiyya.

Amirul Hajj ya buƙaci Alhazan da su ci gaba da yi wa shugabanni addu’a tare da neman zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasa. Ya kuma roƙe su da su ƙara yawaita addu’o’i a Masallacin Harami domin Allah Ya kawo ƙarshen matsalar tsaro da sauran ƙalubalen da ke addabar Najeriya.
Ya gode wa Alhazan kan addu’o’in da suke yi, tare da ƙarfafa musu gwiwa su ci gaba da yi wa jihar da ƙasa baki ɗaya addu’ar samun bunƙasar tattalin arziki a sauran kwanakin zamansu a Makkah.

Shi ma da yake jawabi, Darakta Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya yaba wa Alhazan bisa bin dokoki da ƙa’idojin Masarautar Saudiyya.
Ya kuma tunatar da su cewa kada su wuce iyakar nauyin kaya da hukumar ta tanada, wato kilo 8 na kayan hannu da kilo 46 na manyan kaya.
Wasu daga cikin Alhazan da suka zanta da Rediyon Najeriya sun gode wa Gwamna Umar Namadi bisa kulawar da yake nuna musu, tare da alƙawarin ci gaba da kasancewa jakadu nagari ga jihar a ƙasa mai tsarki.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa tawagar gwamnati da ta raka Amirul Hajj ta haɗa da Shugaban Kwamitin Hajji na Majalisar Dokokin Jihar, wasu mambobin Majalisar Zartarwa ta Jiha da sauran manyan jami’ai.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai7 days agoGwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya
