Ilimi
Shugaban Kasa Na Yiwa Al’ummar Musulmi Barka Da Sallah

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya yi kira ga daukacin ‘yan Najeriya da su hada kansu su dukufa wajen gina kasa mai inganci.
Shugaban ya yi wannan roko ne a lokacin da yake taya al’ummar musulmi murnar sallah karama wanda ke nuna karshen watan Ramadan, mai alfarma da ke jaddada cikakkiyar mika wuya ga Allah Madaukakin Sarki da kuma umurninsa na sadaukarwa da hidima ga bil’adama.
A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar, an bayyana cewa shugaban ya yi addu’ar Allah ya karba addu’o’i da sadaukarwa kowa da kowa a wannan Ramadan
Shugaban ya kuma yi fatan za a yi koyo da darussan da aka samu a wannan wata mai albarka,.
Bello Wakili/Wababe
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
