Labarai
Hajj2026: An Yi Kyakkyawan Tanadi ga Alhazai a Minna da Filin Arfa- Labbo
Daga Usman Muhammad
A yayin da ake shirye-shiryen fita Mina don gudanar da aikin hajjin bana, Jukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa tace ta gamsu da tsarin da hukumomin kasar Saudiyya suka yi na Tantinan Alhazai a Mina da kuma Arafa.
Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka ga wakilinmu Usman Mohammed Zaria a Birnin Makkah.

Yana mai cewar Hukumar Aikin Hajji ta kasa NAHCON, ta gayyaci hukumomin Alhazai na jihohi domin ziyarar masaukan Alhazai a Mina da Arafa, wanda suka duba tare da gamsuwa da tsarin saukar da Alhazan.
Yace an baiwa jihar jigawa kason ta wadda ya kunshi bangaren maza daban, na mata daban.

Alhaji Ahmed Umar Labbo yayi nuni da cewar akwai alama da aka manna na nuna bangaren jihar jigawa.
Kazalika, yace ya sa a kara bugo wasu shaida wato sticker da za a manna a bangarorin biyu don Alhazan su rika gane tentinsu cikin sauki.

A don haka, yayi kira ga Alhazan da su kasance masu hakuri da juriya a yayin zaman su a Mina, tare da bin umarnin shuwagabannin Hukumar Alhazan don kwalliya ta biya kudin sabulu.
Labbo, ya kuma ja hankulan su game da tsafta a masaukan da kuma ban dakuna, da ma da harabar da aka kebe masu.

Yayi kira a gare su da su jajirce matuka wajen gudanar da addu’o’i ga kananan hukumomin su da jihar Jigawa da ma Najeriya baki daya.
Shi ma Darektan tsare-tsare tsare na hukumar kuma shugaban Kwamitin sufuri, Alhaji Sabo Aujara yace sun ziyarci Mina da Arafat da Muzdalifa, tare da nuna gamsuwa da ci gaban da aka samu.
Arab, yace an kuma nuna musu hanyoyin da za su bi na Alhazan Najeriya domin kaucewa cinkoso da dai sauran su.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
