Labarai
Rundunar ’Yan Sandan Taraba Ta Cafke Wanda Ake Zargi Da Damfara
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba ta sanar da al’umma kama wani da ake zargi da aikata laifukan sojan gona da damfara da kuma karɓar kuɗi ta hanyar yaudara, inda yake ikirarin yana da alaƙa da Ofishin Gwamnan Jihar Taraba.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar mai riƙon muƙami, ASP Victor Mshelizah, ya sanya wa hannu.
Sanarwar ta ce, a ranar 12 ga watan Mayun 2026 da misalin ƙarfe 11:30 na safe, mataimakin jami’in tsaron Gwamnan Jihar Taraba (ADC) ya samu sahihan bayanai cewa wasu mutane marasa gaskiya na amfani da sunansa da ofishinsa wajen bata masa suna tare da damfarar ’yan siyasa da sauran jama’a a jihar.
Ta ce bayan samun bayanan sirrin, jami’an tsaro suka fara bincike domin gano tare da cafke waɗanda ke da hannu a cikin ayyukan damfarar.
Sanarwar ta ƙara da cewa, bayan gudanar da bincike mai zurfi, an kama wani mai suna Seth Samuel Sule, mazaunin unguwar Magami a ƙaramar hukumar Jalingo ta jihar Taraba, bisa zargin hannu a lamarin.
A yayin tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa laifinsa da kansa, inda ya bayyana cewa tsakanin ƙarshen watan Afrilun 2026 zuwa farkon watan Mayun 2026, ya yi amfani da wata lambar waya wajen kwaikwayon ADC na gwamnan jihar Taraba.
Har ila yau, wanda ake zargin ya amsa cewa ya damfari wani mutum kuɗi har Naira miliyan 1 da dubu 320, ta hanyar yi masa alƙawarin taimaka masa wajen samun tikitin takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya a jam’iyyar APC, wanda daga baya aka gano cewa yaudara ce.
Rundunar ta ce har yanzu bincike na ci gaba, kuma za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala binciken.
Rundunar ’yan sandan jihar Taraba ta gargaɗi jama’a da su yi hattara da mutanen da ke ikirarin su jami’an gwamnati ne ko kuma suna da alaƙa da masu riƙe da muƙaman gwamnati domin damfarar mutane.
Ta kuma shawarci jama’a da su riƙa tantance duk wata mu’amala mai muhimmanci ko ikirarin siyasa ta hanyoyin hukuma kafin su bayar da kuɗi ko yin wata yarjejeniya.
Sanarwar ta ƙare da cewa rundunar ’yan sandan jihar Taraba ƙarƙashin jagorancin kwamishinan ’yan sanda, CP Morkwap Sebastian Dongshal, na ci gaba da jajircewa wajen yaƙi da duk wani nau’in damfara da aikata laifuka a faɗin jihar.
Daga Sani Sulaiman.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
