Labarai
Katsina Ta Samu Mutum 105 Da Ake Zargin Sun Kamu Da Cutar Sanƙarau
Hukumomin lafiya a jihar Katsina sun shiga shirin ko-ta-kwana bayan da aka samu mutum 105 da ake zargin sun kamu da cutar sanƙarau, wadda ake danganta yaɗuwarta da tsananin zafi a lokacin rani.
Babban Sakataren Hukumar Bunƙasa Kiwon Lafiya ta Matakin Farko a jihar, Dakta Shamsuddeen Yahaya, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai bayan taron duba halin da ake ciki kan cutar.
Ya ce an samu rahoton bullar cutar a ƙananan hukumomi 20, musamman Katsina, Jibiya, Kaita, Mani, Mashi, Zango da Musawa waɗanda suka fi yawan masu alamun cutar.
Dakta Yahaya ya ce gwamnati tare da haɗin gwiwar abokan hulɗarta sun ɗauki matakan daƙile yaɗuwar cutar, inda aka sanya sassan sa ido da bayar da amsa a cibiyoyin lafiya cikin yanayin gaggawa.
A cewarsa, jami’an sa ido daga matakin jiha zuwa ƙananan hukumomi da al’umma suna aiki tare domin gano duk wani wanda ake zargi da kamuwa da cutar tare da ba shi kulawar gaggawa.
Ya ce duk da tsananin zafi da sauran abubuwan da ke ƙara haɗarin kamuwa da cutar, matakan da aka ɗauka sun taimaka wajen rage bazuwarta.
Sai dai Dakta Yahaya ya ce har yanzu ba a tabbatar da rasuwar kowa sakamakon cutar ba, yana mai kira ga jama’a su gaggauta kai rahoton duk mai fama da zazzaɓi mai tsanani, ciwon kai ko taurin wuya.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta tanadi magunguna tare da horas da ma’aikatan lafiya domin tunkarar cututtukan da kan bulla a lokacin rani kamar sanƙarau.
Haka kuma ya ce jihar ta samu tallafi daga Hukumar Yaƙi da Cututtuka ta Najeriya NCDC ta hanyar horas da jami’an lafiya da samar da ƙarin magunguna da kayan gwaje-gwaje.
Isma’ila Adamu/Katsina
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai7 days agoGwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya
