Labarai
An Bayyana Rasuwar Jalul Baba Ahmed A Matsayin Babban Rashi
An bayyana rasuwar marigayi Barrista Jalul Baba Ahmed a matsayin babban rashi ga iyalansa da ma’aikatan Radio Nigeria Kaduna da kuma abokan arziki da masoyansa.
Shugaban Hukumar Ilimin Sakandare ta jihar Neja, Alhaji Abdulkadir Shehu Nafuntua, ne ya bayyana haka cikin saƙon ta’aziyyar da ya aikewa Radio Nigeria Minna.
Ya ce rasuwar marigayin abin takaici ne matuƙa, yana mai cewa zai yi wuya a samu gurbin da zai cike gibi da ya bari saboda ƙwarewarsa da jajircewarsa wajen aiki.
Alhaji Abdulkadir Shehu Nafuntua ya yabawa irin yadda marigayin ke fassara labarai da gabatar da shirye-shirye da sharhi cikin kwarewa da nagarta.
Ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin da ma’aikatan Radio Nigeria Kaduna tare da addu’ar Allah ya gafarta masa kura-kuransa ya kuma sanya shi a Aljannatul Firdausi.
Aliyu Lawal/Minna
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
