Labarai
Jirgin Farko na Maniyyatan Jihar Sakkwato Ya Isa Kasa Mai Tsarki
Daga Nasir Malali
Rukuni na farko na maniyyatan jihar Sakkwato ya isa Masarautar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026.
Amirul Hajj na jihar kuma Ministan Kwadago da Ayyuka, Alhaji Muhammadu Maigari Dingyadi, ya bayyana cewa jimillar Alhazai 484 ne jirgin kamfanin Aquiline Airline ya dauka daga Filin Jirgin Sama na Sultan Abubakar III da ke Sakkwato.
Wakilin Rediyon Najeriya a Sakkwato ya ruwaito cewa jirgin da ke dauke da maniyyatan ya tashi da misalin karfe shidda da kwata na safiyar yau Litinin 11 ga watan Mayun 2026.
Maniyyatan sun fito ne daga kananan hukumomin Wamakko, Tambuwal, Tureta, Shagari, Sabon Birni, Isa da Dange/Shuni na jihar.
Da yake jawabi ga maniyyatan kafin tashinsu, Mataimakin Gwamnan jihar Sakkwato, Idris Muhammad Gobir, ya bukace su da su kare martabar jihar Sakkwato da Najeriya baki daya, ta hanyar nuna halaye nagari a duk tsawon zamansu a kasar Saudiyya.
Bikin kaddamar da tashin maniyyatan ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, malamai, jami’an filin jirgin sama da mambobin kwamitocin aikin Hajji daban-daban, wadanda suka taru domin shaida tashin jirgin tare da yin addu’o’in samun nasarar gudanar da aikin ibadar.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
