Labarai
Kebbi Ta Samu Ci Gaba Kan Mata
Gwamnatin Jihar Kebbi ta ce ta samu gagarumin ci gaba wajen ƙarfafa mata da kare haƙƙin yara da tallafa wa marasa galihu.
Kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban yara, Hajiya Halima Hassan Kamba, ta bayyana haka yayin taron manema labarai a Birnin Kebbi. Ta ce gwamnatin Gwamna Nasir Idris ta aiwatar da shirye-shiryen horas da mata da matasa sana’o’i domin dogaro da kai da rage talauci.
Hajiya Halima ta ƙara da cewa ma’aikatar ta samar da tallafi ga marayu ta hanyar ba su kuɗaɗe da kayan sana’a domin su fara ƙananan sana’o’i. Ta kuma yaba da gudunmawar matan gwamna wajen tallafa wa shirye-shiryen ƙarfafa mata da matasa a jihar.
Sani Haruna/Kebbi
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
