Labarai
2027: Zan Dora Kan Kyawawan Ayyukan Marigayi Sanata Godiya Akwashiki – Silas Agara
Tsohon Darakta Janar na Hukumar Samar da Ayyukan Yi ta Ƙasa, National Directorate of Employment, Silas Ali Agara, ya ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓensa domin neman kujerar Sanatan Nasarawa Ta Arewa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Da yake jawabi a wajen taron da aka gudanar a Akwanga, tsohon mataimakin gwamnan ya ce ya yanke shawarar shiga takarar ne bisa kiraye-kirayen da jama’a da masu ruwa da tsaki suka yi masa domin ya ba da tasa gudunmawar wajen ci gaban yankin.
Agara ya bayyana cewa yana da cikakken shiri da ƙwarewar shiga zaɓen fidda gwani da kuma babban zaɓe, idan har al’ummar yankin suka ba shi goyon baya domin ya wakilce su a majalisar dattawa.
Ya yabawa marigayi Godiya Akwashiki, wanda ya wakilci yankin a majalisar dattawa, yana mai cewa ya gudanar da ayyuka masu yawa kafin rasuwarsa, musamman wajen samar da ababen more rayuwa, ƙarfafa matasa da mata, ilimi da koyar da sana’o’i.
Silas Agara ya yi alƙawarin ɗora kan kyawawan ayyukan da marigayin ya fara tare da ƙaddamar da sababbin shirye-shirye domin jama’a su ci moriyar dimokuraɗiyya da ingantacciyar shugabanci.
Ya ce ikon mulki daga Allah yake, kuma yana neman amincewar jama’a domin ya wakilce su yadda ya kamata, tare da gode musu kan ƙauna da goyon bayan da suke nuna masa.
A cewarsa, daga cikin mazaɓu 35 na yankin sanatocin Nasarawa ta Arewa, sun zaɓi mutum 266 a matsayin tubalin yaƙin neman zaɓensu, waɗanda ya ce an zaɓe su ne bisa nagarta da ƙwarewar siyasa.
Agara ya kuma yi alƙawarin tafiya da kowa tare da tabbatar da cewa ba zai yi watsi da al’umma ba idan ya samu nasara.
A nasa jawabin, Darakta Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen, Mohammad Usman Aya, ya buƙaci haɗin kai da jajircewa daga masu ruwa da tsaki domin cimma burinsu.
Haka kuma ya buƙaci al’ummar jihar Nasarawa da su tabbatar sun karɓi katin zaɓe domin zaɓar shugabanni nagari da za su kawo ci gaba ga al’umma.
Aliyu Muraki/Lafiya
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
