Labarai
Majalisar Dokokin Kano Ta Tabbatar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamna
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tabbatar da Murtala Sule Garo a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan jihar, bayan nasarar tantance shi da aka yi.
An tabbatar da shi ne bayan gabatar da rahoto da kuma amincewa da shi daga wani kwamitin wucin gadi yayin zaman majalisar da Kakakin Majalisar, Jibril Isma’il Falgore, ya jagoranta.
Da yake gabatar da rahoton, shugaban kwamitin kuma Mataimakin Kakaki, Muhammad Bello, ya ce an naɗa Garo ne bayan murabus ɗin tsohon Mataimakin Gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo.
Ya bayyana cewa an gudanar da tantancewar ne bisa tanadin Sashe na 191(3)(c) na Kundin Tsarin Mulkin Nigeria na 1999 (wanda aka yi wa gyara), wanda ke bai wa majalisa damar amincewa da wanda aka naɗa idan gurbi ya samu.
Kwamitin ya ce an yi wa Garo cikakken tambayoyi kan ilimi, ƙwarewa a aikin gwamnati, fahimtar mulki, da kuma hangen nesansa ga ci gaban jihar. Haka kuma an binciki takardunsa da kyau.
Kwamitin ya ƙara da cewa Garo ya nuna cikakkiyar fahimta game da aikin da ke gabansa tare da gabatar da tsari mai kyau da zai taimaka wa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen aiwatar da manufofinta.
Bisa wannan rahoto, majalisar ta amince da nadin nasa, wanda daga baya aka kada ƙuri’a kuma dukkan ‘yan majalisa suka amince da shi baki ɗaya, inda aka tabbatar da shi a matsayin Mataimakin Gwamnan Kano.
Majalisar ta kuma jaddada aniyarta na ci gaba da haɗin gwiwa da bangaren zartarwa domin tabbatar da shugabanci nagari, rikon amana, da ci gaban jihar.
Khadijah Aliyu/Kano
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
