Labarai
Jam’iyyar ADC A Katsina Ta Zaɓi Sabbin Shugabanni
Jam’iyyar ADC reshen jihar Katsina ta zaɓi sabbin shugabanninta, inda aka zaɓi Alhaji Mohammed Rimi a matsayin shugaban jam’iyyar na jihar, sai Mansur Mu’azu a matsayin mataimaki, Mukhtar Adahama a matsayin sakatare, yayin da Amina Lawal ta zama shugabar mata.
An zaɓi shugabannin ne yayin taron babban zaɓen shugabannin jam’iyyar na jihar, wanda ya haɗa masu ruwa da tsaki da wakilai daga mazaɓu 361 da shugabannin jam’iyya daga matakan jiha da ƙananan hukumomi, tare da wakilai daga hedikwatar jam’iyyar ta ƙasa.
A yayin rantsar da sabbin shugabannin, jigo a jam’iyyar, Mustapha Inuwa, ya gargaɗi mambobin jam’iyyar da su yi taka-tsantsan da masu neman haddasa rikici a cikin jam’iyyar gabanin zaɓen 2027.
Ya buƙaci mambobin jam’iyyar da su kasance masu haƙuri da biyayya tare da mayar da hankali wajen ƙarfafa tubalin jam’iyyar, yana mai cewa al’umma na ƙara nuna goyon baya ga jam’iyyar.
Haka kuma ya buƙaci hukumar zabe ta kasa da ɓangaren shari’a su tsaya tsayin daka wajen kare ‘yancin kai da tabbatar da bin doka domin dorewar dimokuraɗiyya.
Wakilin hedikwatar jam’iyyar ta ƙasa, Lawal Batagarawa, ya yaba da yadda aka gudanar da zaɓen cikin adalci, sannan ya roƙi mambobi da su fifita muradun jam’iyya fiye da na kansu domin samun haɗin kai.
Tun da farko, shugaban kwamitin zaɓe, Babangida Talau, ya bayyana cewa an yi amfani da tsarin sasanci wajen zaɓen shugabannin, kamar yadda dokokin zaɓe suka tanada, tare da raba muƙamai bisa daidaito tsakanin yankunan sanatoci uku na jihar.
Sauran jiga-jigan jam’iyyar sun buƙaci sabbin shugabannin da su sake farfaɗo da jam’iyyar tare da ƙarfafa ta a matakin ƙasa domin samun nasara a zaɓen 2027.
Isma’ila Adamu/Katsina
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai7 days agoGwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya
