Labarai
Gwamnatin Tarayya Na Shirin Kaddamar Da Sababbin Shirye-Shiryen Rage Talauci A Najeriya
Gwamnatin Tarayyar Nigeria ta bayyana aniyarta na ƙaddamar da wani sabon shiri na kyauta da zai taimaka wajen fitar da ‘yan ƙasa daga talauci cikin tsari mai ɗorewa.
Ministan Harkokin Jin-ƙai da Rage Talauci, Dr Bernard Doro, ne ya bayyana haka yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma waɗanda suka ci gajiyar shirin tallafin kuɗi na HOPE-CT, wanda aka gudanar a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.
Ya ce manufar shirin ita ce tantance yadda tallafin gwamnati ke kawo sauyi a rayuwar gidaje marasa galihu. A cewarsa, a ƙarƙashin shirin HOPE-CT, jihar Kwara ta samu kusan naira miliyan 13.7, yana mai bayyana jihar a matsayin abar koyi wajen aiwatar da shirin.
Ministan ya yaba da yadda shirin ya kai ga al’umma a matakai daban-daban, tare da jinjinawa gwamnan jihar AbdulRahman AbdulRazaq kan jagoranci da kulawar da yake bai wa walwalar jama’a.
A nata jawabin, Kwamishiniyar Jin-ƙai da Ci Gaban Jama’a ta jihar, Dr Mariam Nnafatima Imam, ta ce shirin ya zo a kan lokaci kuma ya yi tasiri matuƙa.
Ta bayyana cewa sama da gidaje dubu 183 ne suka amfana da tallafin a matakai uku na farko a dukkan ƙananan hukumomi 16 na jihar.
Ta ƙara da cewa shirin ya yi daidai da manufofin gwamnatin jihar wajen tallafa wa marayu da yara marasa galihu da masu nakasa da tsofaffi da sauran marasa ƙarfi, tare da inganta cibiyoyin kula da yara.
Wasu daga cikin waɗanda suka ci gajiyar tallafin naira dubu 75,000, sun ce sun saka kuɗin ne cikin sana’o’in sayar da POP da gawayi, tare da gode wa gwamnatin tarayya bisa tallafin da ta bayar.
Sun kuma roƙi gwamnati da ta faɗaɗa shirin domin ƙarin mutane su samu damar cin gajiyarsa.
Muhammad Rabiu/Kwara
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
