Labarai
NSCDC Ta Gargadi Masu Laifi Da Barayin Kadarori A Kwara
Hukumar tsaro ta NSCDC a jihar Kwara ta gargadi masu aikata laifuka da masu lalata kadarorin gwamnati da su kauce wa jihar.
Sabon kwamandan hukumar, Abbas Mohammed, ya bayyana haka a cikin wani saƙo da ya aikewa al’ummar jihar, inda ya jaddada kudurin hukumar na kare rayuka da dukiyoyi da kuma kiyaye muhimman kadarorin ƙasa.
Ya ce rundunar za ta ƙara ƙaimi wajen amfani da hanyoyin tattara bayanan sirri domin yaƙi da dukkan nau’o’in laifuka, tare da ɗaukar matakan rigakafi kafin aukuwar su.
Kwamandan ya kuma nuna cewa jihar Kwara ba za ta zama mafakar masu laifi ba, yana mai cewa a shirye suke su yi amfani da dukkan dabarun tsaro domin tabbatar da zaman lafiya.
Haka kuma, ya buƙaci al’umma da su kasance cikin shiri tare da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai a kan lokaci domin taimakawa yaƙi da aikata laifuka.
Muhammadu Rabi’u/Kwara
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
