Connect with us

Kasuwanci

‘Yan Kasuwar Albasa a Najeriya Sun Dakatar da Fitar da Kaya Zuwa Ghana

Published

on

Daga Nasir Malali 

’Yan Kasuwar Albasa a Najeriya sun dakatar da fitar da albasa zuwa Jamhuriyar Ghana sakamakon wani sabani da aka samu.

A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da shugabannin kungiyoyin ’yan kasuwar albasa suka fitar a Sakkwato,  wadda aka rabawa manema labarai, sun ce wannan mataki ya biyo bayan yawaitar hare-hare da ake kai wa ’yan kasuwarsu, musamman a kasuwar Kotoku, wacce take muhimmiyar cibiyar kasuwanci ce a babban birnin Ghana.

A cewar ’yan kasuwar, lamarin ya kara kamari ne bayan wata takaddama tsakanin ’yan kasuwar Najeriya da na Ghana wadda ake zargin ta kai ga kwace manyan motoci dauke da albasa mallakar ’yan kasuwar Najeriya.

Wannan lamari, wanda ke barazana ga wani muhimmin bangare na kasuwancin noma a yankin kasashen Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma ECOWAS, ya janyo damuwa kan tsaron ’yan kasuwar Najeriya da kuma dorewar harkokin kasuwancin kan iyaka tsakanin kasashen biyu.

Sanarwar ta kara da cewa dakatarwar za ta ci gaba da kasancewa har sai an warware dukkan matsalolin da ke akwai tare da dawo da yanayi na kasuwanci mai aminci, adalci da bin doka.

Ta kuma yi kira ga hukumomin da abin ya shafa a Najeriya da Ghana, tare da kungiyoyin yankin, da su gaggauta binciken abubuwan da aka ruwaito, ciki har da kwace motocin albasa na ’yan Najeriya, domin hana sake faruwar irin wannan rikici a nan gaba.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara