Labarai
Gwamnatin Zamfara ta Jinjinawa Hukumomin Tsaro Bisa Wanzar da Zaman Lafiya a Jihar
Daga Aminu Dalhatu
Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana jin daɗinta tare da yaba wa hukumomin tsaro da ke aiki a jihar bisa nasarar da suka samu a yaƙi da rashin tsaro, musamman a wani sabon samame da ya kai ga hallaka kimanin ’yan bindiga 100.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Mahmud Mohammed Dantawasa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce wannan nasara hujja ce karara ta ƙwazo da ƙwarewar jami’an tsaro, waɗanda ke ci gaba da sadaukar da rayukansu domin kare al’umma a sassan jihar.
A cewarsa, gwamnatin jihar na matuƙar yaba wa sadaukarwarsu da jajircewarsu wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Zamfara.
Mahmud Dantawasa ya ƙara da cewa wannan nasara babbar alama ce ta ci gaba a ƙoƙarin da ake yi na rushe ƙungiyomasu’yan ta’adda, da kawar da barazanar ’yan bindiga da ta addabi yankuna da dama na jihar.
Ya jaddada cewa gwamnatin jihar na ƙarfafa gwiwar jami’an tsaro da su ci gaba da zama jajirtattu, da ci gaba da aiki tuƙuru.
Gwamnatin ta kuma tabbatar musu da cikakken goyon baya da kuma ci gaba da ba su tallafin kayan aiki, tare da yin kira agare su da kada su yi ƙasa a gwiwa har sai an tabbatar da tsaro a dukkan sassan jihar.
Haka kuma, gwamnatin jihar ta sake jaddada aniyarta ta ƙarfafa haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya da dukkan masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, tare da alƙawarin ci gaba da bayar da duk wani tallafi da ake buƙata domin nasarar ayyukan tsaro a yanzu da ma nan gaba.
A ƙarshe, kwamishinan ya yi kira ga al’ummar Zamfara da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro haɗin kai ta hanyar ba da bayanai a kan lokaci da kuma kula da tsaro a cikin al’umma.
-
Labarai4 days agoRukunin Farko na Maniyyatan Jihar Jigawa Ya Tashi Zuwa Kasar Saudiyya
-
Labarai2 days agoJihar Jigawa Ta Kammala Jigilar Alhazai Zuwa Kasa Mai Tsarki
-
Labarai4 days agoRukunin Farko na Alhazan Jihar Kebbi ya Isa Kasa Mai Tsarki
-
Kasuwanci2 days agoBOA da Majalisar Wakilai za su Samar da Injinan Noma a Dukkan Mazabu
-
Labarai5 days agoKashim Shettima Ya Kaddamar da Jirgin Farko na Maniyyatan Najeriya
-
Labarai2 days agoGwamna Bago Ya Umurci SEMA Ta Gaggawata Kai Tallafi ga Wadanda Iftila’in Guguwa ya Shafa a Mokwa da Bida
-
Ilimi2 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Yaba wa Ministar Harkokin Mata Kan Inganta Rayuwar Al’umma
-
Labarai4 days agoGwamnan Jigawa Ya Bukaci Alhazai Su Yi Addu’ar Zaman Lafiya da Ci Gaban Najeriya
