Labarai
Kwara: Shugabannin APC na Mazabu 52 sun amince da Abdulrazaq a takarar Sanata 2027
Shugabannin ƙananan hukumomi na jam’iyyar APC a yankin Kwara Ta Tsakiya sun amince gaba ɗaya da Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq a matsayin ɗan takarar Sanata mai wakiltar mazabar a zaɓen 2027.
Shugabannin Ward 52 ne suka bayyana haka yayin ganawa da ‘yan jarida a Ilorin ƙarƙashin inuwar kungiyar Sugabbanin Mazabun APC, wanda shugaban su, Alhaji Abdullahi Baba Gobir, ya jagoranta.
Sun ce Abdulrazaq ya fi kowa sanin bukatu da muradun al’ummar yankin Kwara Ta Tsakiya, kasancewarsa ɗan asalin yankin kuma mai kusanci da jama’a.
A cewarsu, wannan goyon baya ya samo asali ne daga ra’ayin tabbatar da jin daɗin jama’a da ci gaban yankin Kwara Central.
Sun ƙara da cewa matakin ya kuma dace da al’adar siyasa ta ba shugabanni damar ci gaba da hidima a mataki mafi girma idan sun nuna ƙwazo a shugabanci.
Shugabannin sun jaddada cewa goyon bayan ba siyasa kawai ba ne, illa dai ra’ayi ne na haɗin kai domin tabbatar da ci gaba da shugabanci nagari da zai amfanar da jama’a a matakin ƙasa.
Ali Muhammad Rabiu/Ilorin
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai23 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
