Labarai
Hukumar Alhazai ta Jigawa ta Hori Tawagar Manema Labarai da Aiki Bisa Gaskiya da Amana
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta buƙaci tawagar kafafen yaɗa labarai ta shekarar 2026 da ta yi bisa gaskiya, haƙuri da jajircewa wajen hidimtawa Alhazan jihar a ƙasar Saudiyya.
Babban Daraktan hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya yi wannan kiran yayin wani taron da tawagar kafafen yaɗa labarai gabanin gudanar da aikin Hajjin bana, wanda aka gudanar a hedikwatar hukumar da ke Dutse, babban birnin jihar.
Ya bayyana cewa wannan aiki amana ce babba wadda ya kamata su jajirce domin sauke nauyin da aka dora musu.
Ya ƙara da cewa aikin ya haɗa da yaɗa bayanai kafin tafiya Hajji, wayar da kai da ilmantarwa, ɗaukar rahotanni, da kuma isar da sahihan bayanai cikin lokaci ga al’ummar Jihar Jigawa da ma ƙasa baki ɗaya kan harkokin Hajji a Najeriya da kuma a Masarautar Saudiyya.
A cewarsa, za a raba tawagar kafafen yaɗa labarai zuwa kwamitoci daban-daban domin tabbatar da nasarar gudanar da aikin Hajjin 2026.
Ya yabawa Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, bisa amincewa da kafa tawagar, tare da kira ga mambobin da su gudanar da aikinsu bisa ƙwazo, rikon amana da kuma tsoron Allah.
Da yake ƙarin haske kan gyaran rabon guraben Hajjin 2026 ga jihohi kamar yadda Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON)) ta umarta, Daraktan ya bayyana cewa Jihar Jigawa ta samu gagarumar nasara wajen shigar da bayanan dukkan maniyyata a shafin yanar gizo kafin wa’adin ƙarshe.
Ya kuma ce hukumar ta kammala gwajin lafiya ga dukkan maniyyatan jihar a babban asibitin gwamnati da ke Dutse, daidai da ƙa’idojin hukumomin Saudiyya.
Labbo ya ƙara da cewa gwajin lafiyar yana da alaƙa kai tsaye da sharuɗɗan bayar da biza ga maniyyatan shekarar 2026.
A nasa jawabin na godiya a madadin mambobin tawagar, Babban Manajan gidan Talbijin na kasa reshen Jigawa(NTA), Malam Muhammad Ibrahim, tare da Malam Lawan Iliya Dutse na Talabijin na Jihar Jigawa, sun yaba wa gwamnatin jihar da hukumar bisa amincewa da guraben tawagar kafafen yaɗa labarai.
Sun kuma yi alƙawarin cewa za su tabbatar da amincewar da aka yi musu ta hanyar gudanar da ayyukansu cikin ƙwarewa, sadaukarwa da kuma tsoron Allah.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
