Connect with us

Labarai

Jigawa: Hukumar Alhazai ta Yaba da Naɗin Sarkin Dutse Amirul Hajjin 2026

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa naɗa Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Hamim Muhammadu Sanusi a matsayin jagoran Alhazan jihar a aikin Hajjin shekarar 2026.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Alhaji Habibu Yusuf Adamu, ya fitar ga manema labarai a Dutse.

Ya bayyana cewa, Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya ce naɗin ya dace ƙwarai, la’akari da jajircewar Sarkin wajen harkokin addini da kuma rawar da yake takawa a matsayin babban jagoran al’umma a Jihar Jigawa.

Ahmed Labbo ya jaddada cewa Amirul Hajj na shekarar 2026 yana da cikakken ilimin addini da ya dace domin jagorantar tawagar jihar.

Ya kuma yi alƙawarin yin aiki kafaɗa da kafaɗa da Amirul Hajjin, tare da neman shawararsa a matsayin jagoran al’umma kan duk wasu lamurra da za su taso yayin gudanar da aikin.

Darakta Janar ɗin, a madadin ma’aikatan hukumar, ya miƙa saƙon taya murna ga Amirul Hajji, tare da tabbatar da aniyar ma’aikatansa na yin aiki tare.

Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya naɗa Sarkin Dutse a matsayin Amirul Hajj domin jagorantar Alhazan jihar zuwa ƙasar Saudiyya a aikin Hajjin shekarar 2026.

 

 

Labarai

Labarai17 hours ago

Sauye-sauyen Da Tinubu Ya Samar Ya Haifar Da Cigaba A Jihohi – Namadi

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matakan da...

Labarai20 hours ago

Jigawa Ta Yi Nazarin Sabbin Tsare-tsaren Masaukin Alhazai A Saudiyya

Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce tana nazarin hanyoyin inganta jin daɗin alhazai...

Labarai2 days ago

Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400

Daga Khadijah Aliyu  Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka...

Labarai3 days ago

Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da...

Labarai3 days ago

Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus

Daga Isma’il Adamu  Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a...

Labarai3 days ago

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu...

Labarai3 days ago

Arewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari

Daga Usman Muhammad Zaria  Daraktan Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce...

Labarai3 days ago

Shettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Shugaba...

Labarai4 days ago

Jigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz

Daga Usman Muhammad Zaria Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da wayar dan...

Labarai4 days ago

Majalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027

Daga Khadijah Aliyu  Majalisar Dokokin Jihar Kano na shirin karɓar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027 daga Gwamna Abba Kabir Yusuf...

Mafi Shahara