Ilimi
An Bukaci Musulmi Su Kula da Maganganunsu
An shawarci Musulmi da su kula da maganganunsu tare da tabbatar da cewa suna faɗar gaskiya a kowane lokaci.
Limamin Masallacin Darul-Khair da ke Ilorin, Jihar Kwara, Imam Abdulmumini Abdulrafiu-Onilaru ne ya yi wannan kira a yayin hudubar Juma’a.
Ya bayyana cewa mutane da dama na amfani da maganganunsu wajen jawo wa kansu da kuma wasu cutarwa.
A cewarsa, kasancewar ana cikin watan Rajab, ana sa ran Musulmi za su fara shirya kansu tun yanzu domin tunkarar watan azumin Ramadan.
Imam Abdulrafiu-Onilaru ya shawarci Musulmi da su rungumi dabi’ar aikata alheri a kowane lokaci, domin samun lada mai kyau daga Allah.
ALI MUHAMMAD RABIU
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
