Connect with us

Labarai

Gwamnatina Ta Gaji Bashin $587m Da N85bn – Gwamna Uba Sani

Published

on

 

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya ce gwamnatinsa ta gaji bashin dala miliyan 587 da bashin Naira biliyan 85 da kuma ayyukan kwangila 115 daga gwamnatin Nasir El-Rufai.

Gwamnan, ya bayyana hakan ne a Kaduna a ranar Asabar yayin da yake jawabi a wajen wani taro, inda ya ce dimbin bashin da ake bin jihar na laƙume abin da jihar ke samu.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ware Naira biliyan bakwai daga cikin Naira billiyan 10 da Gwamnatin Tarayya ta ware mata a watan Maris, domin biyan bashi.

Gwamna Sani ya koka kan tashin farashin canji, wanda ya ce jihar na biyan kusan ninki uku na bashin da gwamnatin baya ta karbo.

Ya Kuma koka da yadda gwamnatin El-Rufai ta bar wa jihar biliyan uku kacal a asusun jihar, wanda ya gaza biyan albashin ma’aikata da ake biya na Naira biliyan 5.2 a duk wata.

Gwamna Sani, ya ce gwamnatinsa ba ta ci bashin ko sisi ba tun bayan wata tara da ya hau mulki, duk da dimbin bashin da ya gada.

“Mun yi nazari cikin tsanaki kan halin da muke ciki. Ina sanar da ku cewa duk da dimbin bashin da muka gada, har zuwa yanzu ba mu ciyo bashin ko kobo ba,” in ji shi.

Gwamnan ya kara da cewa muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba sun hada da tsaro, samar da gidaje, ilimi, kiwon lafiya, da tallafa wa masu kananan sana’o’i.

Ya ce gwamnatinsa za ta kuma mayar da hankali wajen samar da ci gaba ta hanyar saka hannun jari, inganta tattalin arziki da samar da gidaje masu sauki.

Una Sani, ya bayyana wasu muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba a 2024 da suka haɗa da tsaro, samar da ababen more rayuwa, bunkasa ilimi, samar da gidaje da ci gaban birane da dai sauransu.

A nasa jawabin, tsohon Babban Hafsan Hafsoshi, Janar Martin Luther Agwai (mai ritaya), ya bukaci a ɓullo da hanyoyin magance matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta, inda ya ce idan ba a samu zaman lafiya da tsaro ba, ba za a iya samun ci gaban da jihar ke muradi ba.

Ya yaba wa gwamnan kan yadda ya rage hanyoyin da kuɗaɗen tafiyar da gwamnati ke zurarewa.

Ya bukaci al’ummar jihar da su guji nuna bambancin siyasa, addini ko kabilanci tare da mara wa gwamnatin jihar baya domin shawo kan kalubalen bashi da ta ke fuskanta.

Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamali, ya yi wa gwamnatin fatan alheri duk da kalubalen da ta ke fuskanta.

Ya kuma kara da cewa gwamnan yana da gogewar da zai inganta tattalin arzikin jihar domin samun ci gaba.

 

 

 

Labarai

Labarai2 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi1 week ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Mafi Shahara