Connect with us

Labarai

An Raba Kayan Agaji Tare da Sake Fasalin Albashin Dagattai a Kauru

Published

on

 

Majalisar Karamar Hukumar Kauru dake Jihar Kaduna ta raba kashi na 2 na kayayyakin tallafin abinci da suka kunshi buhunan masara da shinkafa 600 kowannensu, a kokarin da gwamnati ke yi na rage wahalhalun da jama’a ke fama da shi sakamakon cire tallafin mai.

Da yake mika ragamar rabon kayayyakin ga Shugabannin kwamitin, wadanda sune zababbun gundumomi 11, Shugaban Karamar Hukumar, Alh Bashir Tanko Dawaki, Ya umurcesu su yi adalci kana su tabbatar kayayyakin sun isa ga mabukata da Marayu da masu lalurar nakasa da gajiyayyun dake gundumomin.

Shugaban Karamar Hukumar Kauru Alhaji Bashir Tanko Dawaki.

Alh Bashir Dawaki ya yabawa Gwamna Uba Sani na tallafin abincin da nufin rage wahalhalun da talakawan yankin ke fuskanta.

Alh Hamisu Umar

Da yake tsokaci a madadin shugabannin kwamitin wadanda suka karbi tallafin gundumomin su, kakakin majalisar kansilolin, Alh Hamisu Umar ya nuna farin cikinsa ga gwamnatin jihar bisa wannan yunkuri, ya sha alwashin zasu raba kayayyakin yadda ya dace

A wata sabuwa kuma, shugaban Karamar Hukumar Alh Bashir Dawaki, Ya sanarda karin albashi ga Dagatai dake daukacin masarautu uku dake fadin karamar hukumar Kauru.

Jami’in yada labarai na Karamar Hukumar, Alh Sani Yahaya, ya furta cewa kodayake shugaban bai fadi yawan karin da aka yi ba, sai dai hakan ya zama wajibi domin karfafa musu gwiwar gudanarda ayyukansu a matsayinsu na jagororin wanzar da zaman lafiya da tabbatarda hadin kai.

 

Bashir Dawaki ya yabawa Dagatai wadanda su ke kusa da al’uma a matakin farko bisa gudunmuwarsu na cigaban yankin, ya bukacesu su kara himma ta hanyar taimakawa jami’an tsaro wajen kawarda miyagun ayyuka a tsakanin al’uma.

 

Ya kuma gargadi masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a yankin, su nemi iznin gwamnati kafin aikata hakan ko kuma su fuskanci hukunci.

 

LR: Dagacen Garin Kagadama sai Kuma Wakilin Raya Kasan Kauru Alh Yusuf Muhammad.

A jawabin Dagacen Garin Kagadama dake gundumar Kauru Alh Umar Kasimu ya nuna jin dadinsa bisa wannan yunkuri ya yi alkawarin cigaba da zage damtse wajen tabbatarda zaman lafiya a yankunansu

 

Yusuf Zubairu Kauru 

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Labarai3 days ago

Majalisar Dattijan Na So A Bai Wa Kananan Hukumomi Yancin Kai

Majalisar Dattijan Najeriya ta nemi Shugaba Tinubu ya shige gaba domin nema wa kananan hukumomi ‘yanci a wajen jihohi, wanda...

Labarai3 days ago

‘Yan Ƙwadago Sun Yi Watsi Da N48,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

  Ƙungiyar Ƙwadago NLC ta yi fatali da tayin naira 48,000 da Gwamnatin Tarayya ta gabatar a matsayin mafi ƙarancin...

Labarai3 days ago

Tinubu Zai Ciyo Bashin $500m Don Sayen Mitocin Lantarki

  Majalisar Dattawa ta sahale wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ciyo bashin Dala miliyan 500 da nufin samar da mitocin...

Ilimi3 days ago

Za A Fara Daukar Masu Sakamakon Jarabawar NECO A Jami’o’in Birtaniya

  Jami’o’in kasar Birtaniya na shirin fara daukar daliban Najeriya masu shaidar jarabawar kammala sakandare ta NECO. Shugaban hukumar shirya...

Labarai4 days ago

Jirgin Farko Na Alhazan Najeriya Ya Tashi Zuwa Kasa Mai Tsarki

A yau Laraba 15 ga watan Mayun 2024 ne jirgin Najeriya na farko ya tashi da Alhazan Jihar Kebbi 423...

Labarai4 days ago

Najeriya Ta Kaddamar da Shafin Intanet Don Samun Bayanai Game da Ma’adinai

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shafin intanet ranar Talata wanda zai bai wa masu zuba jari damar samun cikakkun bayanai...

Labarai5 days ago

Tsohon Lauyan Trump Ya Ce Ubangidansa Ya Ba ‘Yar Fina-finan Batsa Toshiyar Baki

Tsohon babban lauyan Donald Trump, Michael Cohen, ya aikata abinda masu gabatar da kara su ka yi ta fatan ya...

Labarai5 days ago

Kotu Ta Yankewa Wani Mutum Hukuncin Zaman Gidan Yari Na Watanni 2 Bisa Satar Doya

Kotun Majistare da ke Gwagwalada a babban birnin tarayya Abuja, ta yanke wa wani mutum mai suna Isah Sani hukuncin...

Labarai5 days ago

Jamhuriyar Benin Ta Haramta Fitar Da Masara Zuwa Nijar

Jamhuriyar Benin ta hana fitar da masara zuwa ƙasashen waje a daidai lokacin da farashin hatsi ya yi tashin gwauron...

Labarai5 days ago

Gwamnatin Kano Ta Nada Ibrahim Garba Shugaban Tawagar ‘Yan Jarida A Hajjin Bana

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da nadin Ibrahim Garba Shuaibu a matsayin shugaban tawagar ‘yan jaridu a aikin Hajjin 2024....

Mafi Shahara