Labarai
Rundunar ‘Yan Sanda Ta Nemi Hadin Kan ‘Yan Jarida A Jigawa
Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Jigawa ta nemi goyon bayan kafafen yada labarai wajen tsara dabarun yaki da laifuka da kuma matsalar shan miyagun kwayoyi a Jihar Jigawa.
Kwamishinan ’yan sanda na jihar, Dahiru Muhammad ne ya yi wannan kira lokacin da mambobin Kungiyar ’Yan Jarida bangaren masu ruwaito labarai a Jigawa suka kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa dake Dutse, babban birnin jihar.
A cewarsa, kafafen yada labarai na taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan al’umma kan harkokin tsaro, tare da fadakar jama’a kan gudunmawar da za su iya bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ya bayyana cewa, baya ga bada rahotannin ayyukan ’yan sanda, kafafen yada labarai na kara gina kwarin gwiwar jama’a ga hukumomin tsaro, wanda hakan ke sa mutane kara sakin jiki don bayar da muhimman bayanai da za su taimaka wajen dakile aikata lailaifuka da gudanar da bincike.

Kwamishinan, wanda aka turo shi kwanan nan zuwa jihar, ya ce zai yi amfani da wani sabon salo wanda zai fi mayar da hankali kan hada kai da al’umma, tare da kirkiro da yanayin da kowa zai bada tasa gudunmawar, musamman a lamuran da suka shafi tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.
Ya kara da cewa, ’yan sanda za su fadada dangantaka da al’umma maimakon harkar tsaro kadai, domin kara gina amintaka da juna.
CP Muhammad ya ce daga cikin matakan da za su dauka sun hada da tabbatar da kwarin gwiwa a tsakanin jama’a, gudanar da bincike da gurfanar da laifuka da gaggawa domin adalci, da kuma karfafa aikin ’yan sanda tare da al’umma.
A nasa jawabin shugaban kungiyar ’yan jaridar, Kwamared Muhammad Zangina Kura, ya ce sun kai ziyarar ce domin karfafa dangantaka tsakaninsu da rundunar ’yan sanda.
Ya ce, tun shekaru da dama akwai kyakkyawar alaka tsakanin ’yan jarida da rundunar a Jigawa, kuma suna da niyyar kara habaka wannan alaka da sabon kwamishina.
Kwamared Kura ya jaddada cewa tsaro nauyi ne na kowa da kowa. Ya kuma tabbatar wa kwamishinan da cewa kungiyar ’yan jarida za ta ci gaba da aiki kafada da kafada da rundunar wajen aiwatar da sabuwar dabarar da ta yi daidai da manufofin Sufeton ’Yan Sanda na kasa, Kayode Adeolu Egbetokun, na tabbatar da hada kai wajen yaki da laifuka da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
