Labarai
Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci FRSC Ta Kara Kaimi Wajen Kiyaye Hadurra A Tituna
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya bukaci Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) da sauran masu ruwa da tsaki da su kara kaimi wajen aiwatar da Tsarin Kiyaye Hanyoyi, yana mai jaddada cewa alkaluman hatsarorin mota da ake samu har yanzu suna nuna cewa kasar na fuskantar manyan kalubale.
Da yake jawabi a wajen taron shekara-shekara na FRSC karo na takwas a Abuja, Shettima ya ce kiyaye lafiyar hanyoyi aiki ne na hadin gwiwa wanda ke bukatar hadin kan gwamnatin tarayya, jihohi, kamfanoni masu zaman kansu da kungiyoyin fararen hula.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta kuduri aniyar kara karfafa tsaro a hanyoyin fadin kasar nan, tare da yabawa FRSC bisa ci gaba da gudanar da ayyukansu cikin shekaru 37 da suka wuce.
A nasa jawabin, Sakataren Gwamnatin Tarayya Sanata George Akume, ya bayyana cewa tsaron hanya muhimmin ginshiki ne na ci gaban kasa, inda ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da tallafawa FRSC ta hanyar horaswa da hadin kai da sauran hukumomi.
Taron ya kuma samu halartar abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa ciki har da FIA Foundation wadda ta yaba da rawar da FRSC ke takawa a fagen kula da hanyoyi.
Masu ruwa da tsaki daga kotuna, jami’an tsaro, jami’o’i da sashen sufuri sun yi alkawarin hada kai wajen magance matsalolin Najeriya musamman yawan mace-macen da ke faruwa sanadiyyar hadurra.
Daga Bello Wakili
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
