Labarai
Rundunar Operation Fansan Yamma Ta Raba Takin Zamani Ga Monoma A Karamar Hukumar Tsafe
A wani yunkuri na kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Arewa maso Yamma da wasu sassan Arewa ta Tsakiya, Kwamandan Rundunar Operation Fansan Yamma, Manjo Janar O.O. Soyele, ya raba buhunan taki 200 ga manoma a karamar hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.
Wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar Kyaftin David Adewusi, ya fitar ta bayyana cewa wannan tallafi an yi shi ne da nufin karfafa amfanin gona da inganta rayuwar al’umma a yankin.

Janar Soyele wanda ya sami wakilcin Kwamandan Sashen Kayayyakin Aiki na Rundunar, Birgediya Janar Nkemakolam Mbaka, ya mika buhunan takin ga Sarkin Tsafe, Alhaji Abubakar Muhammad Bawa, a matsayin wani bangare na shirin kyautata hulɗa tsakanin sojoji da al’umma, na Hedikwatar Tsaro.

Janar Soyele ya bayyana cewa wannan shiri na hanyar sulhu ba tare da amfani da karfi ba an yi shi ne domin bunkasa harkar noma, karfafa hulɗar sojoji da al’umma, da kuma ƙarfafa manoma su koma gona, a daidai lokacin da ake gudanar da samamen kawar da barazanar tsaro a yankunan noma.

Kwamandan ya kuma gode wa Sarkin Tsafe, gwamnati da al’ummar Jihar Zamfara bisa goyon bayan da suke bayarwa wajen yaki da ta’addanci da ’yan bindiga.
Ya shawarci manoma da su yi amfani da takin yadda ya kamata domin samun karin amfanin gona.

A nasa jawabin, Sarkin Tsafe, Alhaji Abubakar Muhammad Bawa, ya gode wa Kwamandan Rundunar bisa abin da ya bayyana a matsayin taimakon da ya zo a kan gaba. Ya ce wannan kyauta za ta inganta samar da abinci da kuma kyautata rayuwar manoma, tare da tabbatar da ci gaba da goyon baya ga sojoji.

Taron ya samu halartar shugabannin al’umma, wakilan shugaban karamar hukumar Tsafe, da kuma jama’ar garin da suka yaba da wannan shiri.
Daga Aminu Dalhatu
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
