Labarai
Majalisa Wakilai Ta Yabi Jihar Jigawa Kan Dorewar Shirye-shiryen Lafiya Ga Kowa
Kwamitin kula da harkokin lafiya na majalisar wakilai ya yaba wa jihar Jigawa bisa kasancewarta jagaba a shirin samar da lafiya ga kowa ta hanyar manyan sauye-sauye da kuma kudaden da ake kashewa wajen kara inganta fannin.
Yabon ya fito ne lokacin da kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Honorable Amos Gwamna Magaji, ya kai ziyarar ban girma ga Gwamna Umar Namadi a gidan gwamnati Dutse.
Hon. Magaji ya bayyana gamsuwa da irin nasarorin da jihar ta cimma musamman wajen ware sama da kashi 15 cikin 100 na kasafin kuɗin shekara-shekara ga harkokin lafiya.

Ɗan majalisar ya kuma taya gwamnan murna bisa nasarar lashe kyautar dala 500,000 na Primary Health Care Leadership Challenge Award, yana mai cewa hakan shaida ce ta irin cigaban da jihar ke samu a tsarin gyaran fannin lafiya.
Hon. Magaji ya kara yaba da matakin gwamnatin jihar na daidaita albashin ma’aikatan lafiya da na tarayya, yana mai cewa wannan zai rage barin ƙwararru su fita ƙasashen waje, wanda hakan zai iya jawo wasu daga sauran jihohi zuwa Jigawa.
A nasa jawabin, Gwamna Namadi ya gode wa ‘yan majalisar bisa yabon da suka yi, tare da jaddada kudirin gwamnatinsa na mayar da fannin lafiya ginshikin cigaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma.

Gwamnan ya jaddada cewa ilimi, da cigaban tattalin arziki, da samar da aiki na iya bunkasa ne kawai idan jama’a suna cikin koshin lafiya.
Ya bayyana cewa gwamnatin sa ta fi mayar da hankali wajen karfafa cibiyoyin lafiya na farko a matsayin ginshikin samar da ayyukan lafiya, tare da shirin kafa wani cibiyar lafiya da za ta ƙunshi cibiyar bincike, cibiyar cututtukan zuciya, da masana’antar iskar taimakawa numfafashi wato oxygen.
Gwamna Namadi ya tabbatar wa kwamitin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da sauye-sauye tare da yin aiki kafada-da-kafada da majalisar tarayya domin cimma burin samar da lafiya ga kowa a jihar Jigawa.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
