Labarai
An Mayar Da Gaza Maƙabarta Mafi Girma A Duniya — EU

Babban jami’in kula da harkokin waje na Tarayyar Turai (EU), Josep Borrell ya bayyana cewa, yaƙin da sojojin Isra’ila ke yi a Gaza ya mayar da yankin ya zama maƙabarta mafi girma a duniya.
“Gaza ta kasance tana da babban gidan yari mafi girma kafin fara yaƙin. A yau ita ce maƙabarta mafi girma a duniya, “in ji Borrell a taron ministocin EU a Brussels.
“Wata maƙabarta ce ga dubun dubatar mutane da kuma maƙabarta ga yawancin muhimman ƙa’idojin dokar jin ƙai.”
Borrell ya kuma sake nanata zarginsa da cewa Isra’ila na amfani da yunwa a matsayin “makamin yaƙi” ta hanyar ƙin barin manyan motocin agaji shiga Gaza.
“Isra’ila na amfani da matakin haifar da yunwa,” in ji shi a wani taron jin ƙai.
Ministan Harkokin Wajen Isra’ila, Isra’ila Katz, ya mayar wa Borrell martani, ya kuma ce masa da ya daina kai wa Isra’ila hari, mu kuma amince da ‘yancinmu na kare kai daga laifukan Hamas.
“Isra’ila ta ba da damar kai agajin jin ƙai mai yawa zuwa Gaza ta ƙasa, da sama da ruwa ga duk wanda ke son taimakawa,” in ji Katz kamar yadda ya bayyana kafar sadarwar zamani X (twitter).
Yaƙin Gaza mafi muni da aka taɓa yi ya ɓarke bayan da Ƙungiyar Hamas ta ƙaddamar da wani harin da ba a taɓa ganin irinsa ba, a ranar 7 ga watan Oktoba wanda ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 1,160 a Isra’ila, galibi fararen hula, a cewar ƙididdigar da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya bayar bisa alƙaluman hukumomin Isra’ila.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
