Labarai
Iyalan Muhammadu Buhari Sun Bayyana Godiyarsu Ga ‘Yan Najeriya Da Sauran Kasashen Duniya
Iyalan tsohon shugaban kasa marigayi Muhammadu Buhari sun bayyana godiya ta musamman ga ‘yan Najeriya da al’ummomin kasashen duniya bisa goyon baya da nuna alhini lokacin rasuwar marigayin.
A cikin wata sanarwa da Malam Garba Shehu ya sanyawa hannu a madadin iyalan, ta bakin Malam Mamman Daura, sun mika godiya ta musamman ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mai dakinsa, Sanata Remi Tinubu, bisa kulawar da suka nuna kafin, da kuma bayan rasuwar tsohon shugaban kasar.
“Irin ziyarce-ziyarcen da aka kai, saƙonnin jaje, da kuma yanke hukuncin ayyana hutu da kuma canza sunan Jami’ar Maiduguri zuwa Buhari, duk sun kasance alamu ne na tausayawa da suka sanya mana kwarin gwiwa ” in ji iyalan.
Hakazalika sun jinjinawa mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, wanda ya yi tafiya zuwa Birtaniya sannan ya kai ziyara Daura tare da wasu ministoci a lokacin makokin. “Hakan ya karfafa mana gwiwa wajen fuskantar wannan babban rashi,” in ji sanarwar.
Iyalan sun kuma gode wa manyan shugabannin duniya, ciki har da Sarki Charles III na Birtaniya, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres, da mataimakiyar Amina Mohammed, Shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka (AU), da shugabannin kasashen ECOWAS bisa jajentawa, wasiku, da ziyarar gaisuwa ko kiran waya.
Sun kuma yaba da ziyarce-ziyarce da sakonni daga shugabannin Najeriya na yanzu da na baya, ciki har da tsofaffin shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar, tsofaffin mataimakan shugaban kasa Atiku Abubakar, Namadi Sambo, Yemi Osinbajo, da Ambasada Babagana Kingibe.
Gwamnonin jihohi daban-daban musamman gwamnan jihar Katsina Dr. Dikko Umar Radda, gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, da tsohon gwamnan jihar Anambra Dr. Peter Obi, duk sun samu yabo bisa irin tausayin da suka nuna.
Sanarwar ta kara da godiya ga shugabannin Majalisar Tarayya ciki har da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, Shugaban Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin, da sauran ‘yan majalisa na matakin kasa da jihohi.
“Har ila yau muna jinjina ga Sarakuna daga sassa daban-daban na Najeriya, ciki har da Nai Alfarma Sarkin Musulmai, Shehun Borno, da sarakunan Gwandu, Katsina, da Daura.”
Iyalan Buhari sun kuma gode wa shugabannin addinai da na al’umma, kungiyoyin matasa, mata, ‘yan siyasa, ma’aikata, jami’an tsaro, da kafafen watsa labarai da suka shiga cikin al’amuran makokin.
Sai kuma manyan ‘yan kasuwa da suka hada da Aliko Dangote, Abdul Samad Rabiu, Muhammadu Indimi, Dahiru Mangal, Kola Adesina, wadanda su ma sun kasance da iyalan marigayin yayin jimamin rashinsa.
Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya jagoranci Najeriya daga shekarar 2015 zuwa 2023, ya rasu a Birtaniya a farkon wannan wata. An binne shi a mahaifarsa ta Daura a jihar Katsina.
Bello Wakili
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
