Labarai
Gwamnan Zamfara Ya Jaddada Bukatar Ganin Alkalai Suna Yanke Shari’a Akan Lokaci
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bukaci sabbin alkalai a jihar da su mayar da hankali wajen hanzarta yanke shari’a a kotuna.
Gwamna Lawal ya bayyana hakan ne a yayin da ya jagoranci rantsar da sabbin alkalai na kotun koli da Khadiman Kotun Daukaka Kara ta Shari’a a fadar gwamnatin jihar da ke Gusau.

Gwamnan ya bayyana cewa an nada alkalan ne bayan tantancewa da kuma amincewar Hukumar Shari’a ta Kasa (National Judicial Council).
“Da fari, ina taya ku murna bisa wannan muhimmin matsayi da kuka samu. Wannan nadin naku na nuni da tabbaci da kuma kwarin gwiwa da fannin shari’a ke da shi a kanku.”

Ya bukaci alkalan da su tabbatar da wannan kwarin gwiwa da aka nuna gare su ta hanyar nuna cikakkiyar kwarewa, gaskiya, rikon amana da adalci a ayyukansu.
“Na kuma yaba da namijin kokari da jajircewar babbar mai shari’a ta Jihar Zamfara kuma Shugabar Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta Jihar, Mai Shari’a Kulu Aliyu OFR, da daukacin tawagarta, bisa yadda Hukumar Shari’a ta Kasa zta amince da dukkan wadanda aka mika sunayensu su kuma aka nada su.”


“Wannan lokaci ne mai matukar muhimmanci ga bangaren shari’a na jihar don goyon bayan kokarin wannan gwamnati wajen inganta rayuwar al’umma. Hadin kai tsakanin bangaren zartaswa da na shari’a yana da matukar muhimmanci wajen cimma nasarorin da ake bukata.”
Dr. Lawal ya kara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bayar da goyon baya ta hanyar samar da dukkan hakkoki, alawus-alawus da kuma ingantaccen yanayin aiki domin bai wa alkalai damar yin aiki yadda ya kamata.

Mai Shari’a Kulu Aliyu, Babbar Alkalin Jihar Zamfara, ce ta jagoranci rantsar da sabbin alkalan uku na kotun koli da kuma khadiman kotun daukaka kara guda uku.
Sabbin alkalai na kotun koli da aka rantsar su ne: Garba Sirajo, Rabi Bashir da Abdullahi Nasir. Sai kuma
Khadiman da sun hada da: Ibrahim Jibril, Muhammad Sanusi Magami da Sha’aban Mansir.
Daga Aminu Dalhatu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
