Kasuwanci
Jami’an Hukumar Kula Da Shige Da Fice Ta Kasa Sun Ziyarci Mai Alfarma Sarkin Musulmi A Sakkwato
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana hukumar kula da shige da fice ta Najeriya a matsayin matakin farko na tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyi a kasar.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin daliban jami’ar Immigration da ma’aikatan kwalejin Sokoto a ziyarar ban girma a fadarsa.
Ya yi kira da a samar da jami’an shige-da-fice don duba bakin haure da ke barazana ga zamantakewa da ci gaban tattalin arzikin kasar.
Ya kara da cewa galibin ‘yan kungiyoyin ta’addanci irin su Lakurawas da Boko Haram ba ’yan Najeriya ba ne.
Jagoran ya bayyana cewa, hukumar shige da fice na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaron kasa ta hanyar amfani da bayanan sirri, tantancewa da kuma yin tambayoyi domin gano tare da kama mutanen da ke da tarihin aikata laifuka, da ‘yan ta’adda, ko kuma wadanda ke haifar da wasu matsalolin tsaro kafin samun damar shiga yankunan kasar.
Jagoran ya kara da cewa, Mai Alframa Sarkin Musulmi a shirye yake a kodayaushe don tallafa wa dukkanin hukumomin gwamnati da ke da alaka kai tsaye ga zamantakewa da tattalin arzikin kasa.
A farkon jawabinsa, mukaddashin kwamandan hukumar kula da shige da fice da ma’aikata ta kwalejin Sokoto Muhammad Mu’azu ya ce makasudin ziyarar shi ne mika godiya da kuma samun nasiha ta uba daga mai Alframa Sarkin Musulmi .
NASIR MALALI
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
