Connect with us

Labarai

An Dakatar Da Shugaban APC A Jihar Nasarawa Bisa Zargin Cin Amanar Jam’iyya

Published

on

Jami’an jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga Mazabar  Gayam dake karamar hukumar Lafia a jihar Nasarawa sun dakatar da shugaban jam’iyyar na jihar, Aliyu Bello, bisa zargin aikata ayyukan cin amanar jam’iyya.

Shugaban mazabar Gayam, Ibrahim Iliyasu ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a Lafia, babban birnin jihar.

A cewar sa, daukar matakin dakatar da shugaban jam’iyyar na jihar ya biyo bayan bincike kan koke-koken da mambobin mazabar suka shigar game da ayyukan cin amanar jam’iyya da shugaban ke aikatawa.

Muna da kwararan shaidu da rahotannin da ke nuna cewa ya fito fili yana tallata dan wata jam’iyya daban, wanda hakan ya sabawa sashe na 21 (1), da na (2), da na(7) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar,” in ji shi.

Muna sanar da dakatar da kai daga mukaminka nan take bisa karfin ikon da kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya bamu a karkashin sashe na 21 (D), (I), (111) bayan shawara da mu ka yi da masu ruwa da tsaki na mazabar,” in ji shi.

Ya bayyana cewa za su aika da sanarwar dakatarwar ga shugabancin karamar hukumar Lafia, kwamitin zartarwa na jihar da kuma kwamitin zartarwa na kasa domin tabbatar da dakatarwar tare da daukar mataki na gaba.

Alhaji Ibrahim Iliyasu ya kuma bukaci shugaban jam’iyyar da ya dakatar da bayyana kansa a matsayin mamba ko jami’in jam’iyyar har sai an kammala dukkan matakan da suka dace.

Dakatarwar ta zo ne jim kadan bayan kakakin jam’iyyar APC na jihar, Otaru Douglas, ya bayyana damuwa kan wani shiri da wani dan takarar gwamna a jam’iyyar ke yi na ganin an sauke shugaban jam’iyyar na jihar.

 

Daga Aliyu Muraki 

 

Labarai

Labarai21 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai24 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara