Labarai
Hukumar Alhazan Jigawa Ta Shirya Taro da Shugabannin Alhazai na Kananan Hukumomi
Hukumar jindadin Alhazai ta jihar jigawa ta gudanar da taro da shugabanin shiyya shiyya da kuma jami’an alhazai na kananan Hukumomi Jihar 27 a shelkwatar hukumar dake Dutse gabannin fara jigailar maniyatan aikin hajjin bana.
A lokacin da yake jawabi, Darakta Janar na Hukumar Alhaji Ahmed Umar labbo ya ce taron yana da muhimmanci kasancewar aiki yayi nisa na fara jigilar maniyata zuwa kasa mai tsarki.
Yana mai cewar, hukumar ta kammala duk wani shiri ga maniyyata domin fara jigilar su zuwa kasa mai tsarki.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya kara da cewar, a lokacin taron da suka gudanar da jami’an sun rabawa shugabanin shiyya-shiyya da jami’an su dukkanin kayayyakin maniyyata da dukkan sauran muhimman abubuwa daya dace.
Game da batun biza kuwa, Labbo yace an kammala yiwa maniyatan biza wadda daga yanzu zuwa kowane lokaci za’a sanar da maniyyatan zuwa sansanin alhazai domin jigilar su zuwa kasa mai tsarki.
A sabili da haka nema, Ahmed Labbo ya bukaci shugabanin shiyya-shiyya da suyi takatsantsan da kayayyakin maniyyata saboda mahimmacin sa.
Darekta Janar na hukumar, ya kuma godewa gwamnatin Jihar bisa tanadin dukkanin Muhimman abubuwa da suka kamata a filin jirgin saman kasa da kasa na Muhammadu Sunusi dake birnin Dutse domin fara jigailar maniyyatan a dan kankanin lokaci.
Kazalika, yace Gwamna Umar Namadi yasha alwashin ci gaba da kyautata jin dadin maniyyatan bana tun daga nan gida Najejriya har zuwa kasa Mai tsarki.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
