Labarai
EFCC Ta Cafke Manyan Motoci 21 Makare Da Kayan Abinci
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta cafke manyan motoci 21 makare da kayan abinci da sauran kayayyaki, wadanda za a tsallaka da su kasashen Chadi, da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da kuma jamhuriyar Kamaru.
A wata sanarwa da jami’in yada labarai da hulda da jama’a na hukumar, Dele Oyewale, ya fitar, ya ce jami’an hukumar shiyar Maiduguri sun cafke manyan motocin a wani samame da suka kai a manyan hanyoyin fita da ke kan titin Gamboru Ngala da Bama a jihar Borno.
Sanarwar ta bayyana cewa, da farko ba a gano kayan abincin ba saboda yadda aka boye su cikin dubara a cikin manyan motocin, sai da jami’an suka zurfafa bincike.
Ya kara da cewa, binciken da aka yi ya nuna cewa, an shirya manyan motocin ne zuwa N’djamena, da Jamhuriyar Chadi, da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma Kamaru, tare da lura da cewa, kamawar da aka yi za ta taimaka wajen dakile matsalar karancin abinci da masu fasa kwauri a fadin kasar ke haddasawa.
A cewar sanarwar, wadanda ake zargin a sun bayyana sunayensu kuma za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Daga Dauda Iliya
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
