Connect with us

Labarai

Abdulaziz Yari Zai Raba Tirelar Abinci 358 Ga Mabukata

Published

on

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar Zamfara ta Yamma, Sanata Alhaji Abdulaziz Yari Abubakar na shirin raba tireloli dari uku da hamsin da takwas  na kayan abinci  ga al’ummar jihar.

 

Shugaban kwamitin yada labarai na kungiyar siyasa ta AA Yari, Alhaji Ibrahim Muhammad Birnin Magaji ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Gusau babban birnin jihar.

 

Sanarwar ta ce, matakin yunkuri ne  na bai wa al’ummar musulmi damar fara azumin watan Ramadan mai zuwa cikin sauki.

 

Da yake karbar rahoton mutane dubu dari biyu da hamsin da za su  amfana da tallafin daga kananan hukumomi daban-daban a ranar Lahadi, 3 ga Maris, 2024 a Gusau, kwamirin rabon gado karkashin jagorancin  Lawal Liman,  ya bayyana cewa za a raba Shinkafa, da Siga da Gero  da Masara, a maimakon Masara kadai da aka raba a baya, saboda  muhimmancin watan Ramadan mai alfarma

 

Ya bayyana cewa sama da kashi casa’in da takwas na kayayyakin an yi nasarar jigilar su zuwa kananan hukumomi daban-daban na jihar, don saukakawa wadanda suka ci gajiyar tallafin.

 

Shugaban ya ci gaba da cewa  mabukata ne kadai za su gajiyartallafin, wadanda suka hada da marayu da zawarawa.

 

Ya kara da cewa, za a fara rabon ne  kafin watan Ramadan, don haka ya bukaci jama’a da su ci gaba da yi wa tsohon Gwamna, jihar da kasa baki daya addu’a.

 

SANI DUTSINMA

Labarai

Labarai21 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai24 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara