Connect with us

Labarai

An Gudanar Da Taron WASA Na Rundunar Sojin Najeriya A Gusau

Published

on

Kwamandan runduna ta 1 ta sojojin Najeriya da ke Gusau, Birgediya Janar Opurum Timothy, ya bayyana  wa al’ummar jihar Zamfara da ma kasa baki daya aniyar rundunar sojojin Najeriya na ci gaba da aiki tukuru domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a karshen taron wasannin rundunar sojojin Najeriya ta yammacin Afirka WASA 2024 da aka gudanar a Gusau.

Taro West African Social Activities WASA wani taro ne na shekara-shekara da rundunar sojojin Najeriya ke shiryawa domin  wasannin gargajiya na wannan  yankin na Afirka.

Taron na shekara-shekara yana tattaro Jami’ai, Sojoji, da iyalansu  cikin annashuwa domin wasannin al’adun da kuma bikin ƙarshen  shekara.

Janar Opurum wanda ya jaddada kudirin rundunar na kawar da ‘yan fashi da kuma dawo da zaman lafiya a Zamfara da yankin Arewa maso Yamma gaba daya, ya yi kira ga sojojin da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu, yana mai jaddada cewa, sadaukarwarsu da  na da matukar muhimmanci wajen samun zaman lafiya mai dorewa.

Kwamandan Birgediya wanda ake yi wa lakabi da “Jar Kunama”, ya yabawa al’ummar Zamfara bisa yadda suke ba da hadin kai, musamman ta hanyar samar da muhimman bayanan sirri, wanda ya haifar da gagarumar nasara.

Tun da farko, Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara, wanda kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Meriga ya wakilta, ya yabawa rundunar sojojin Najeriya da sauran jami’an tsaro bisa namijin kokarin da suke yi na samar da zaman lafiya mai dorewa a fadin jihar ta Zamfara.

Taron WASA na bana a Gusau ya samu halartar manyan baki da suka hada da sarakunan gargajiya da shugabannin sauran hukumomin tsaro kamar rundunar sojojin saman Najeriya da jami’an tsaro da dai sauransu.

Muhimman abubuwan da suka faru a wajen taron sun hada da, baje kolin al’adu da raye-raye, wasan kokowa, da dai sauransu.

Yayin da wasu da dama da suka yi nasara suka je gida da kyaututtuka daban-daban da suka hada da man girki, shinkafa da sauran kyaututtuka.

Daga Aminu Dalhatu

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara